Header Ads

FALALAR SAHABBAI

KADAN DAGA CIKIN JAN AIKIN DA SAHABBAI SUKA YI NA YADA ADDINIBAYAN WAFATIN MA'AIKI (SAW): 1- Manzon Allah (sallalLahu alaihi wa sallama) yana yin wafati, sai yawancin wadanda suka karbi musulunci a tsibirin larabawa suka yi ridda, bayan kuma Ma'aiki bai yi wafati ba sai da yawancin garuruwan tsibirin larabawa sukarissina suka mika wuya ga addinin musulunci. Abin da zai nuna hakan shine masu Sirah sun bayyana yawan wadanda suka yi hajjin ban kwana tare da shi da cewa adadinsu ya zarta mutum dubu dari. 2- Farkon jan aikin da Abubakar Siddiq (RA) ya fuskanta shine: yakar 'Yan ridda, Allah ya bashi nasarar ganin bayansu, kwarjinin addinin musulunci ya dawo. Bayan cikin gida ya gyaru, sai ya juya waje, domin ci gaba da isar da sakon Ma'aiki SallalLahu alaihi wa sallama. Wanda tuni Ma'aiki SAW ya fara shimfidar hakan ta hanyar tura wasiku zuwa duk wani Sarki cikin sarakunan kafirci,yana kiransu zuwa addinin musulunci. Abubakar Siddiq (RA) ya kasa rindinar musulunci kashi biyu: Kashi na daya suka doshi kasar Iraq a karkashin jagorancin Khalidbnil Waleed, sun samu nasarar bude kudancin Iraq a lokacin. Kashi na biyu kuma sun nufi kasarSham da jagorancin Yazeed bn Abi Sufyan, da Shurahbeel bn Hasanah, da Mu'awiya, da Amru bnil As, sun samu nasarar bude Sham a yakin "Yarmuka" wanda ya faru a lokacin da Abubakar Siddiq (RA) shi kuma ya yi wafati. 3) A zamanin Umar bnil Khattab (RA) [13 – 23 AH]: Mu'awiya (RA) ya yaki Rumawa, yabude Jazeerah, da Armeniya, da Azrabeejan. 'Iyadh bn Ganam ya shiga gumurzun yaki har yakai (Bahr Qazween) (Wanda kogi ne da kasashe biyar a yanzu suke kewaye da shi: Russia, Iran, Azrabejan, Turkumanistan da Kazakhastan). Amru bnil As ya bude Misra, a lokacin har rundunar musulmai sun kai gefen kasar Libiya suka shiga Tripoli, da Barqah. A can Iraqi kuma Sa'd bn Abi Waqqas ya jagoranci bude garuruwan da suka ragu, bayan ya yi kaca-kaca da rundunar farisawa a yakin Qaadisiyyah, ya murkushe gaba dayan jagororinsu. Musulmai suka ci gaba da kutsawa iyakokin kasar Iran, suka bude Khurasaan, da Ahwaz, da yankin Farisa, suka kara nausawa kudanci har sai da suka kai Makran da kuma kan iyakar garin Sind (Pakestan). Suka kuma nausa gabas har sai da suka bude Sijistaan (Afganistan). (Wannan duk a zamanin Umar RA)kenan. Mu'awiya (RA) ya nemi izini daga Umar (RA) ya kutsa cikin kogi, donyakar wadanda garuruwansu suke haure, amma Umar ya hana saboda hadarin da yake tattare dahakan. 4) A zamanin Halifa Usman bn Affan (RA) an kara bude Khurasan,da Armeniya, da Azrabejan saboda sun nuna kiriniya da bijirewa. A zamaninsa kuma a ka bude: Ray, da Hamzan, da Dabristaan, da Jurjan, aka karasa bude gaba dayan Iran. Aka halaka sarki na daular Farisa wato Yazdajirdu bayan ya karade duniya yana ta guje-guje. A can Sham kuwa 'yan garuruwa ne kadan suka ragu wadanda suke karkashin daular Rumawa suma Mu'awiya (RA) ya karasa bude su. A zamanin Usman (RA) har wayau ya bayar da izinin a kutsa ta kan kogi don yin Jihadi, ba tare da bata lokaci ba, sai Mu'awiya (RA) ya sanya tsarin rindina kashi biyu:Masu Jihadi a lokacin Zafi, da MasuJihadi a lokacin sanyi, ya yi wannan tsarin ne don a ci gaba da yakar Rumawa ba yankewa. A shekara ta (27 Ah) ya samu nasara a kan Rumawa har sai da ya isa kasar Qustantinia = Constantinople (Istanbul) ya kewayeta. A garin Akka da take hannun Israel a yanzu Mu'awiya ya gina ma'aikatar kera Jiragen ruwan yaki (Naval fleet), kuma aka ci nasarar kera babban jirgin ruwanyaki na farko a musulunci, manufarsa itace kutsawa kasashen turawa kamar su Cyprusda take kudu maso gabashin turai, da Arwaad da take kusa da garin (Tarsus) ta cikin Syria. A Misra kuma rindinar musulunci ta ci gaba da nausawa yamma, tana kutsawa kasashen Afrika, karkashin jagorancin Abdullahi bnSa'd bn Abi Sarh, inda ya karya rindinar Rumawa da jagorancin (Gregorius), ya bude garuruwa arewacin Africa har ya dangana da garuruwan kasar Moroco. 5) A lokacin Aliyu bn Abi Talib (RA)saboda fitina da ta kunno kai a garuruwan musulmai, ba a samu an ci gaba da bude-bude ba, tun da sai gida ya gyaru sannan za'a gyara waje. WADANNAN BUDE-BUDEN DUK ANSU SAHABBAN MA'AIKI NE SUKA JAGORANCE SU KUMA DUKA-DUKA AN YI SUNE A CIKIN SHEKARU 25 KACAL. WADANNE IRIN MUTANE NE ZASU IYA KWATANTA IRIN WANNAN MURGUJEJEN AIKIN? KUMA IDAN AN BUDE GARI FA, BA WAI SHIKE NAN BA, A'A AKWAI MALAMAI A CIKIN SAHABBAI DA AKETURA SU GARURUWA, SU KUMA AIKINSU SHINE SU KARANTAR DA MUTANEN GARIN AL'AMURAN ADDININ MUSULUNCI. MAYAKA NE, KUMA MALAMAI NE; TA HAKA ADDININ MUSULUNCI YA YI YADUWAR DA BAI TABA IRINTA BA. LALLAI ALLAH YA YI GASKIYA: (Kun kasance al'uma mafi alheri da aka fitar wa mutane: kuna umarni da [aikata] alheri, kuma kuna hani ga mummunan aiki, kuma kuna yin Imani da Allah). [Aal Imran: 110]. Allah ya saka musu da alheri, ya kara yarda a gare su, ya bamu ikon yin koyi da koyarwarsu, ya hada fuskokimmu tare da su a aljanna. Ameen Ya rabbal 'Alameen.

No comments

Powered by Blogger.