MU'UJIZAR DA ALLAH YA BAWA ZUCIYA..
: Natsu tsaf ka karanta mu'ujizar zuciya... : 1=> Har yanzu ba'a sami master key din da zai iya bude kofar zuciya ba, idan kaga so ya shiga zuciya to mai zuciyar ne ya bude masa kofa har ya sami damar shiga. : 2=> Har yanzu ba'ayi na'urar data fi zuciya sauri ba, zuciya ce ke tafiyar miliyoyin kilomita a cikin second guda. : 3=> Har yanzu ba'a sami na'urar data fi zuciya iya sinsino sinadarai ba, koda baka taba zuwa wani waje ba to zuciyarka ta taba zuwa, da zarar an ambaci wajen nan take zuciyarka zata hararo ma siffar wajen. : 4=> Har yanzu ba'a sami waje wanda yafi ko'ina iya boye sirri ba kamar zuciya. Acikin zuciya ake boye so tsawon lokaci, haka nan acikinta ake boye ki tsawon lokaci. : 5=> Har yanzu ba'a sami gabar data fi kowacce gaba amfani ba a jikin dan adam kamar zuciya, da zarar zuciya ta bar aiki, to dukkan jiki ma zai bar aiki... : Tsarki ya tabbata ga mahaliccin zuciya. : Shi yasa Annabi (s.a.w) yayi gaskiya, da yace: acikin jiki akwai wata tsoka, idan ta gyaru to dukkan jiki ya gyaru. Idan kuma ta baci to dukkan jiki ya baci.... : Muna rokon Allah ya kara mana son Allah da manzonsa a zukatanmu ya kuma tsarkake mana zukatanmu...
No comments