Header Ads

MACEN DA TAFI ALKHAIRI DA WADDA TAFI SHARRI

lallai mafarkin kowani Xa namiji dangane da aure ko samun matar da zai yi rayuwa da ita, bai wuce, Ya samu matar da zai samu nitsuwa da ita, wacce take sonsa, ta kuma damu da shi, mai bashi kulawa a ko da yaushe. Kuma lallai idan Mutane suka nazarci ayoyin Alqur'ani mai karimci da hadisan Annabi ( ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ ) za su ga cewa lallai NASSOSHIN sun yi bayanin sifofin MACE TAGARI; abar neman MASU HANKALI, da cewa itacemai sifar: RIQO da addini, da qoqarin baiwa Allah haqqoqinsa da kuma miji, Haka kuma sun nuna cewa itace: Saliha, mai xa'a, bayan kasancewarta Musulma, ko Mumina. Mace tagari ta kan zama mai gaskiya, da haquri, mai sallah, da azumi, da sadaka ko zakka, mai yawan ambaton Allah, tare da yin biyayya wa mijinta, da kiyaye farji daga alfasha, da kuma kiyaye dukiyar mijinta daga tozartawa, da kuma iyalansa. Har wani hadisin ya nuna cewa, Mace ba za ta lazimci waxannan aiyukan ba face ta shiga aljannar Ubangijinta, a indaAnnabi (ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ) yake cewa: " ﺇﺫﺍ ﺻﻠﺖ ﺍﻟﻤﺮﺃﺓ ﺧﻤﺴﻬﺎ، ﻭﺻﺎﻣﺖ ﺷﻬﺮﻫﺎ، ﻭﺣﻔﻈﺖ ﻓﺮﺟﻬﺎ، ﻭﺃﻃﺎﻋﺖ ﺯﻭﺟﻬﺎ، ﻗﻴﻞ ﻟﻬﺎ: ﺍﺩﺧﻠﻲ ﺍﻟﺠﻨﺔ ﻣﻦ ﺃﻱ ﺃﺑﻮﺍﺏ ﺍﻟﺠﻨﺔ ﺷﺌﺖ ". Ma'ana: "Idan Mace ta yi sallolinta guda biyar, ta yi azumin watanta guda xaya, ta kuma kiyaye farjinta, sannan ta yi biyayya wa mijinta, Sai ace da ita: Ki shiga aljanna daga qofar da kika ga dama daga cikin qofofin aljannah" [Musnad Ahmad, lamba: 1661, Hadisi ne, hasan]. Kuma don qoqarin taqaicewa Mutane sifofin Macen da tafi alkhairi Wassu masu hikima da ilimi sun dunqule sifofin irin wannan matar cikin maganganunsu taqaitattu masu fasaha. Kamar yadda suka yi bayanin wacece asharariyar Mace, Xaya daga cikinsu yana cewa: 1) Itace: Take yardar da Ubangijinta ( ﺗﺮﺿﻲ ﺭﺑﻬﺎ(. 2) Take kuma shagwavar da Mijinta ( ﺗﺪﻟﻞ ﺯﻭﺟﻬﺎ(. 3) Kuma bata barin zaman gidanta ( ﻻ ﺗﻔﺎﺭﻕ ﺑﻴﺘﻬﺎ(. 4) Kuma tana yin sallolinta guda biyar ( ﺗﺼﻠﻲ ﺧﻤﺴﻬﺎ(. 5) Kuma bata fitar da sirrinta ( ﻻ ﺗﺨﺮﺝ ﺳﺮﻫﺎ(. 6) Kuma ba a ganin takalminta ( ﻻ ﻳﺮﻯ ﻧﻌﻠﻬﺎ(. 7) Kuma ba a jin sautinta ( ﻻ ﻳﺴﻤﻊ ﺻﻮﺗﻬﺎ(. 8) Kuma ba a sanin siffarta ( ﻻ ﻳﻌﺮﻑ ﻭﺻﻔﻬﺎ(. 9) Mai izza a cikinMutanenta ( ﺍﻟﻌﺰﻳﺰﺓ ﻓﻲ ﻗﻮﻣﻬﺎ(. 10) Mai jin qasqanci a karan-kanta (ﺍﻟﺬﻟﻴﻠﺔ ﻓﻲ ﻧﻔﺴﻬﺎ). 11) Ga xanta qarami; Mai shayar da shi ne, Mai rarrashinsa ( ﻟﻮﻟﻴﺪﻫﺎ ﻣﺮﺿﻌﺔ ﺣﺎﻧﻴﺔ(. 12) Gidanta kuma aljanna ce, da abin tsinkanta suke a kusa (ﺑﻴﺘﻬﺎ ﺟﻨﺔ ﺩﺍﻧﻴﺔ). 13) Idan ta samu wani alkhairi daga Mijinta sai ta yi godiya (ﺇﻥ ﻭﺟﺪﺕ ﻣﻦ ﺯﻭﺟﻬﺎ ﺧﻴﺮﺍ ﺷﻜﺮﺕ( . 14) Idan kuma ta ga wani sharri a wurinsa sai ta yi haquri (ﻭﺇﻥ ﺭﺃﺕ ﻣﻨﻪ ﺷﺮﺍ ﺻﺒﺮﺕ). 15) Idan kuma ya shigo wurinta sai ta yi farin ciki tana murmushi ( ﺇﻥ ﺩﺧﻞ ﻋﻠﻴﻬﺎ ﺳﺮﺕ ﻭﺗﺒﺴﻤﺖ(. 16) Idan kuma ya fita daga gidanta sai ta yi baqin ciki, tana yin bege ( ﺇﻥ ﺧﺮﺝ ﻣﻦ ﺑﻴﺘﻬﺎ ﺣﺰﻧﺖ ﻭﺗﺸﻮﻗﺖ(. 17) Idan yayi fushi da ita sai ta jure ta yi haquri ( ﺇﻥ ﻏﻀﺐ ﻣﻨﻬﺎ ﺗﺤﻤﻠﺖ ﻭﺗﺤﻠﻤﺖ). 18) Idan ta fiskanto shi sai ta burge shi ( ﺇﻥ ﺃﻗﺒﻠﺖ ﻋﻠﻴﻪ ﺃﻋﺠﺒﺘﻪ(. 19) Idan kuma baya tare da ita to sai ta kiyaye shi ( ﺇﻥ ﻏﺎﺏ ﻋﻨﻬﺎ ﺣﻔﻈﺘﻪ( . 20) Idan ta ga aibinsa sai ta voye ( ﺇﻥ ﺭﺃﺕ ﻋﻴﺒﻪ ﺳﺘﺮﺗﻪ(. 21) Idan ya nemi ta yi masa uzuri sai ta karvi uzurinsa ( ﺇﻥ ﺍﻋﺘﺬﺭ ﻣﻨﻬﺎ ﻋﺬﺭﺗﻪ). Da aka tambaye shi kuma, Wacece mai sharri a cikin Mata, Sai yace: 1. Itace: Mai yawaita rashin lafiya ( ﺍﻟﻤﻤﺮﺍﺽ(. 2. Mai yawaita haila ( ﺍﻟﻤﺤﻴﺎﺽ(. 3. Wacce take kuka ba tare da sababi ba ( ﺍﻟﺘﻲ ﺗﺒﻜﻲ ﻣﻦ ﻏﻴﺮﺳﺒﺐ(. 4. Mai kuma yin dariya ba tare da an samu abinda yake sanya al'ajabi ba ( ﻭﺗﻀﺤﻚ ﻣﻦ ﻏﻴﺮ ﻋﺠﺐ(. 5. Idan zata fita sai ta yi ado, ta kuma bubbuxe jiki ( ﺇﻥ ﺧﺮﺟﺖ ﺗﺒﺮﺟﺖ ﻭﺗﻜﺸﻔﺖ( . 6. Idan kuma ta shiga; sai ta yankwane, ta bubbushe ( ﺇﻥ ﺩﺧﻠﺖ ﺫﺑﻠﺖ ﻭﺗﻘﺸﻔﺖ). 7. Maganarta mai ciyo ne ( ﻛﻼﻣﻬﺎ ﻭﻋﻴﺪ(. 8. Sautinta kuma mai tsanani ne (ﻭﺻﻮﺗﻬﺎ ﺷﺪﻳﺪ). 9. Tana bubbune kyawawa ( ﺗﺪﻓﻦ ﺍﻟﺤﺴﻨﺎﺕ(. 10. Sai kuma ta riqa yaxa munana ( ﻭﺗﻔﺸﻲ ﺍﻟﺴﻴﺌﺎﺕ(. 11. Kuma bata yin haquri akan musibu (ﻭﻻ ﺗﺼﺒﺮ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﻨﻜﺒﺎﺕ). 12. Tana ta makon zamani akan Mijinta ( ﺗﻌﻴﻦ ﺍﻟﺰﻣﺎﻥ ﻋﻠﻰ ﺯﻭﺟﻬﺎ(. 13. Shi kuma, Bata taimakonsa akan zamanin (ﻭﻻ ﺗﻌﻴﻨﻪ ﻋﻠﻰ ﺍﻟﺰﻣﺎﻥ). 14. Idan ya shiga, sai ta fita ( ﺇﻥ ﺩﺧﻞ ﺧﺮﺟﺖ(. 15. Idan kuma ya fita, sai ta shiga ( ﻭﺇﻥ ﺧﺮﺝ ﺩﺧﻠﺖ(. 16. Idan ya kusance ta sai ta gudu ( ﺇﻥ ﻗﺮﺑﻬﺎ ﻧﻔﺮﺕ(. 17. Kuma, ga abokin zamanta (miji) Mai butulci ne (ﻭﻟﻌﺸﻴﺮﻫﺎ ﻛﻔﺮﺕ( . 18. Kuma idan ta yi fushi sai ta yi fajirci (ﺇﺫﺍ ﻏﻀﺒﺖ ﻓﺠﺮﺕ). 19. Xanta a koyaushe yana cikin yunwa ( ﻃﻔﻠﻬﺎ ﺟﺎﺋﻊ(. 20. Farillarta kuma, abar tozartawa ce (ﻭﻓﺮﺿﻬﺎ ﺿﺎﺋﻊ). 21. Ubangijinta yana Mai fushi ( ﺭﺑﻬﺎ ﻏﻀﺒﺎﻥ(. 22. Shi kuma Mijinta, yana ta nadama ( ﻭﺯﻭﺟﻬﺎ ﻧﺪﻣﺎﻥ(. 23. Kuma "Shexan" yana sonta (ﻭﻳﺤﺒﻬﺎ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ). 24. Tana kai kuka, alhalin itace Mai zalunci ( ﺗﺸﺘﻜﻲ ﻭﻫﻲ ﻇﺎﻟﻤﺔ(. 25. Tana yin shaida, alhalin bata wurin ( ﻭﺗﺸﻬﺪ ﻭﻫﻲ ﻏﺎﺋﺒﺔ(. 26. Tana kuma yin zargi alhalin itace mai aibin (ﻭﺗﺬﻡ ﻭﻫﻲ ﻋﺎﺋﺒﺔ). 27. Harshenta yana da tsayi ( ﻟﺴﺎﻧﻬﺎ ﻃﻮﻳﻞ(. 28. Tufanta kuma, gajere ne (ﻭﺛﻮﺑﻬﺎ ﻗﺼﻴﺮ). 29. Shi kumagidanta, tana qaurace masa ( ﻭﺑﻴﺘﻬﺎ ﻫﺠﻴﺮ(. 30. Zancenta qarya ne ( ﻗﻮﻟﻬﺎ ﺯﻭﺭ(. 31. Shi kuma hawayenta na fajirci ne ( ﻭﺩﻣﻌﻬﺎ ﻓﺠﻮﺭ(. 32. An jarrabe ta da, azabar rami, da tavewa ( ﺍﺑﺘﻠﻴﺖ ﺑﺎﻟﻮﻳﻞ ﻭﺍﻟﺜﺒﻮﺭ(. 33. Da kumamanya-manyan al'amura (ﻭﻋﻈﺎﺋﻢ ﺍﻷﻣﻮﺭ). [Duba littafin / Almustaxraf fi kulli fannin Mustazraf, shafi 463-464]. Ni da Ku gabaxaya; Allah ta'alah ya azurta mu, da mafi alherin Mata, Ya kuma tsare mu daga sharrinsu.

1 comment:

Powered by Blogger.