Header Ads

SAKAMAKON ALKAIRI 1***2

Wane irin yunwa kike yafe da itane Ummukalsum? na sani idan ma har da matsalar da kika dorawa kanki qarin tagomashin abin da rashin cin wadataccen abinci. wanda ba kan kowa zan dora laifinba sai kanki. kin kasa bawa zuciyarki salama ki zauna da abokanan zamanki lafiya. duniya ai yar sannuce. sannu ake binta ba da hanzari ba. Nafi kowa sanin ciki dai bai dinki Ummukalsum. cike kike da gaggawa da hanzari cikin alamarinki. baki da hakuri kibi komai da tsari cikin salama aah sau tari kikan dage akan raayinki ki kuma tilastawa duk wani da ya rabeki amincewa da abin da zuciyarki ta saka miki. Shikenan don Allah kada kice min komai a tattare da zamanki da abokanan zamanki. kinzo ne kawai mu gaisa mu sa miki albarka kaman sauran yan uwanki hakan nake fata a koyaushe. ba fuskantar mu da matsala ba. harma kika tilastawa zukantanmu fargaba a duk lokacin da muka yi ido hudu dake. Rana zafi inuwa kuna zuciyarta ta shiga kai komo harma ba ta san lokacin da ta fitar da kwallaba Mama a duniya idan ban fada miki damuwataba wa zan bayyanawa? hakan ce ma tasa nima bana so na kasance mai cin naman dan uwana. Tadin zamanku da abokanan zamanku ba komai bane face cin diddigensa. Shikenan mama nayi shiru. ai daman bance komaiba. Allah dai ya bani hakuri da juriya irin yadda kike min fata ko yaushe mama. Yauwa to ai kinga ko haka shine abu mai alfanu ko ba komai Abdulrashidu zabi ne na kashin kanki Ummukalsum. Tabi mamanta da kallo da nufin fassaro abubuwa da yawa. kada dai har yanzu mamanta tana dubanta da wannan abun? Ya dubeta ya watsar tamkar yana kyamatar ganinta. ita dinma ta yakice shi ta wuce abinta. bayi ta wuce ta saki shawa ta jika jikinta sosai. ta dauro alwala ta gabatar da sallah ta kimtsa cikin bular rigar bacci ta mutanen kasar sin. A lokacin ne ta shiga samawa cikinta abinda zata ci. kasancewar ala tilas an mata kutungwilar korar mai taimaka mata. tace taji ta gani za taci gaba da kulawa da bukatunta. kasancewar tana da madogarar da take samu (albashi). hakan bai masa ba yace baya son shimfida masa iko a gida na kashin kansa. ba ra ayinsa bane ra ayine na tauraruwarsa da nufin kyautata mata. mama tace tayi hakuri wanda hakan ba karamin kwara bane a gareta. Wayewar gari ma tayi wanka tayi ficewata gaba gadi zuwa ofis ba tare da ta tsinka masa ba bare a nemi kai ruwa rana sabida umarnin da ya bata. shikenan daga rana irin wannan ta shiga daukan wannan matakin. lamarin da ya dada nisanta tsakaninsu. Tun tashinta ta kasance a dakin girki kasancewar ranakun karshen mako ne babu aiki. Tayi nisa wajen kokarin harhada gashin kazar mutanen Asia. tabi illahirin jikin kazar ta shafe da hadin maggi da kayan kamshi ta kai hannu da nufin bude mabudin tanderun gashin (oven) caraf dijangala tasha gabanta da itama take kokarin tura kayan gashin. gashin na uwar gijiyartane. Ummukalsum ta dubeta cike da lalaci me kenan dije? Ta yamutsa fuska gami da zumbura baki. Hajiya ta umarta a gasa mata kifi naga kuma kina kokarin tura zabuwarki. Ta rasa kalmar furtawa tana duban dije a lokaci guda ta shiga kokarin tura zabuwarta cikin tanderun gashin aiki dijangala ta babbake ta kare. da alama so take su gwada dantse. Das das.... ta sauki daga matattakalar benen. takalmin kafafunta kadai ya isa duba bayan kyawun da lallausan leshin yayiwa fatar jikinta mai tarin hasks. kai kace da ka lotsa fatar jikinta jini zai balle. Cike da gadara da nuna halin ko in kula tace Me kenan haka dije? me ya kai damo fadawa garken kura? bayan shi da hakuri aka sanshi. kura kam da handama tayi fice a kai. kowa ya kwan da sanin haka. Dije ta rusuna tana bawa uwargijiyarta ba asin magana Ahaf ai na fadi ki cikin dabbobi kura tai musu zarra wajen hadama da babakere ga shegen son kai da zalama... Ta dubeta sosai babu wani shayi ko shakka tace Ban son tanka miki kasancewar Bebi ce sa ar yina kin gane? banda haka da nayi kuli kulin kubra dake. amma duk da hakan bari na mika sako ga Bebi gagara duniya. ta hanun jinin jikinta tarwatsa duniya ciki harda iyalin dr shitu da Hauwa u (Bebi) matarsa yar mutanen bakin iyakar najeriya da kasar chadi. Wani abu ne wannan da ya tarwatsa wannan iyalin? ehem tambayar kenan malama Hanan maza yi hanzari ki mikata ga Bebi sisi legas yayar Hanan kilakin jami ar bayaro. Tas taji saukar mari a kuncinta. ba tayi wani mamakiba. tace eh aikin kai ne duk da cewa komai kyawun yabanya daga tsiro aka samar da ita. ban ko mance da wannan tsiron ba mai tarin gurbata muhalli. Amma bari kiji ko Bebi tayi min wannan kaskancin bana iya kauda kai duk da kasancewar na sani tasha hada dantse da maza Ta fincikota ta zura mata mari ta kuma kara zura mata wani marin. Ummukalsum ta rufe idanunta ta huce da yawa daga cikin takaicin da yarinyar ta guma mata. daman ita mai zafice in banda rayuwa mai ake da tarin sauyi mai Hanan ta isa a gurinta?. Ya gama kidemewa ya gama razana. Zan fice nabar maka gidan inbar maka yaranka muradinka kenana ko? Bazan zauna waccar juyar tayi wa iyayena hasarata ba. Ya janyota sosai ta shiga kokarin fincikewa. Na gaya maka zan fice inbar maka gidan kai da Ummukalsum shikenan ko abinda kake muradi? Zan dau matakin da bakya tsammani. kiyi hakuri dai ki fahimceni Hanan idan kika saka kafafu kika fice a gidan nan kibarni dawa? kice dukkanin farin cikin Rashid ya datse. Hanan itace cika makin farin cikin Rashid. duba daya ya kan yi mata yaji duk wani kunci dake tattare dashi ya rushe. ya gushe baki dayansa. sabida tarin kauna da begen da yake mata. Da wannan furucin ya shawo kanta. saidai ta zuba ido da matakin da zai dauka akan Ummukalsum. Ya rufe idanunsa ya dankara mata muggan kalamai na rashin kyautatawa irin dai yadda ya saba. Har abada keda ruskar farin ciki mamugunciya mai kyashi da samun dan uwanta. burinki ki nakasta min mata , me za ai da mace juya saidai taci ta kasayar ? kai tur ! da kasantuwarki karkashin inuwata Ummukalsum. Ta dubeshi sosai cike da ban mamaki , bawa kenan mai tarin makuwa , wannan kalma ke fita daga bakinka Abdulrashid? Ta gyada kai , babu mamaki ga tarin sakamakon da bawa yakan ruska daga wurin bawan da ya jima da kyautatawa harma ya zamo silar sabbaba mishi al amura da yawa. Ya galla mata wani mugun kallo, ba nazo ne kiyi min dogon sharhiba, kashedi da jan kunne na karshe a gareki , babu hujjar da zaki nemi nakasta min yara, ki kuma juyo kan uwarsu sabida kina bakin ciki da samun dan uwanki. Ta juma wannan abu nai mata suya a zuci , idan har kowa zai mata wannan gorin , bai kyautu Abdulrashid ya zamo daga cikinsu ba , idan har da kara da halacci Abubuwa da yawa sunci gaba da faruwa , irin yadda aka saba , kwarai tana kokarin kaucewa abinda zai iya kawo musu matsala, musamman ta bangaren madafi nan ne kadai ya zamo wurin hadakarsu , takan bada baya har zuwa lokacin da zata kammala hidindiminta koda yake galibi hadimanta ne ke aiwatarwa. Cike da gadara ta kunno kai falon , koda yake tilas sai ta fara ratsewa ta sassan uwargidan kafin wucewa sassan gwanartasu , amarya Hanan da yayansu can saman benen gidan. Ummukalsum na gefen kujera jamila ta gallo mata wani mugun kallo tana taunar cingam kas kas na yaran tsan tsan rashin arziki. Ta fara taku jikin matakalar da zata sada ta da sassan Hanan jar fata balarabiyar yayansu. Ummukalsum tabi ta da kallo , tana rayawa jamila kenan ? lallaikam kowane gauta jane , idan har ire iren su jamila zasu ci gaba da yi mata wannan diban karan mahaukaciya , al umman da ta jima da hidimtawa ? Suna tare da yayanta ta ruske su kasancewar ranakun karshen mako ne , fuskarta ta fadada tayi kamar ta saba jamila a kafada saboda tsabar kulawa. Ya kika baro su hajiya ? ina samira da autanmu balarabe ? Ta zauna sosai, hajiyar cema tace inzo in duba mata surkarta mai kulawa da al amarinta, mai kulawa da al amuran iyalinta. Hanan tayi murmushi, jamcy kenan kikan manta surukuwar ta hajiya ba guda bace ? Anan jamila ta bata rai , ta maida dubanta ga yayanta yana tsaka da kurbar lemon dabino da zuma (date with honey drink) da Hanan dinsa ta sabar masa. Babban yaya kayi min aikin gafara , kiris ya rage mu janye kafafunmu daga muhallinka , matarka muraran tana nuna kyashin ganin sawunmu a muhallin dan uwanmu , nayi kamar zan juya sabida kaskancin da ta nemi gwada min yanzunnan kafin in shigo , mu da muhallin dan uwanmu amma bamu da wata izza a cikinsa ? ba a dubanmu a bakin komai bare a daukemu da muhimmanci. Banyi tsammanin banda albarkacin Hanan ba , akwai wanda zai juri bin sawunka sabida rashin nagartar matarka. Ya ajiye kofin gilashin a lokacin da yai wa lemon kyakykyawan zuka , dukda tarin zakinsa kamar madaci yake kwankwada sabida tarin dacin da Ummukalsum ke shayar dashi. ya kwan da sanin lamarin ba kansa kadai ya tsayaba har da yan uwansa. Kiyi hakuri jamila , tana ganin cewa ita din wata tsiyace a gurina take aiwatar da duk wani abu da ranta ya biya mata , babu ko shakka ina gab da daukan matakin da za a raba garin kowa yaja nasa. Ya fice da nufin gangarowa kasa domin bin ba asin tozarcin da take nufin yiwa yan uwansa. Hanan ta dubeta zuciyarata tai mata dadi, saidai tayi kokarin dannewa. Kina damun kanki akan kucakar matar can , ni ai ko duba bata isa a idanunaba , balle har ta saka shamaki a tsakanin yan uwa na Rasheed da nake jinsu tamkar jini da tsoka a gareni. Ta yunkura uhm... bari dai ki gani kanwar mai gidan mai take da bukata in kawo mata ? akwai gasasshiyar kaza da duminta , akwai farfesun hanta da koda.... kai bari dai kiga , sai abinda kanwar maigida ta zaba ta darje. Lokaci guda teburin abincin dake gaban jamila ya gama tumbatsa da kayan kwalam da makulashe, da irin wannan kirkin amarya Hanan ta saye zukatan dangi na Rasheed, ciki kuwa harda hajiyarsa. Cikas din kawai duk abinda za a aiwatar dashi ba domin lillahi ba , bashi da wani alfanu , haskensa yakan tsayane kadai ga wanda kayi shi , wataran ma ya zama sai labari hasken ya gushe , babu abinda yai saura face duhu. Ta jima tana nazarin abin da za ta girka,ba ta ko son fitowa madafin girkin sabida zuwan Jamila,hakan zai iya kawo mata matsala. Bata taba jurar wulaqanci,lamarin da ya kan sa ta kasa kau da idanunta,har a kai ga qoqarin kai ruwa rana a tsakaninsu,musamman irin wannan lokaci Hanan ta kan yi amfani da damarta. Yunwa na nuqurqusarta,ta yi zamanta abinta ta gaji da shan kayan zaqi,bare ta tsotsi lemo ko madara a firjinta.Mai dan nauyi kawai ta ke da buqata,babu kuma halin hakan,don kaucewa matsala aqalla mamanta da sauran 'yan uwanta kunnuwansu sa huta da kai komon tarin laifukanta,kawai sai ta ji hawaye na zubo mata. Madafinta? Madafin da ita da hannunta ta zana,ta tsara yadda zai kasance? Amma a yau ya gagare ta? Ya gagari sahunta,waccan rayuwar nan mai inganci,tuni ta rushe ta zama sai labari. A wannan lokaci da ake tsaka da bikin Samira 'diyar Hajiyar su Rashid, ta kau da kai daga duk wani batanci daga abokiyar zamanta da 'yan kanzaginta,tai uwa tai makarbiya da al'amuran bikin Samira ba ta yi zaton ko Jamila da suka fito ciki daya ba tana da bakin fada a ji irin na amarya Hanan ba. Kocokom al'amuran bikin a qarqashin ikonta ya ke a nan cikin gidansu ake tsaka da cin dabdalar shagali mai cike da neman jan magana. Tana da zafin zuciya,ba ta iya kau da kai ta qyale lamarin da a qarshe akan aza laifin a kanta,mafitar guda ce,ta wuce ta bar gidan matsala kamar yadda ta lanqaya masa. Kamar sau daya ta je wurin Hajiyar ta yi mata fatan alheri,ta miqa mata nata alherin,zamanta a nan din ma ba komai ba ne face matsala. Hajiyar ta bi yarima ana kan ganiyar shan kida da ita,don haka sai kaffa-kaffa da kaucewa abinda zai iya kawo mata matsala a tsakinsu,ko ba komai uwa- uwa ce,ko wane da ko yana so a girmama tasa bata tunkari gidansu ba,ta sani sarai maman za ta dora laifin a kanta,na rashin son a zauna lafiya da abokan zamanta,bayan ko hakan shine maslaha a tsakaninsu,ta wuce gidan yar uwarta,Zainabu mai biye mata,gidanta yana nan a 'Shagari Ktrs'suka sha hirar su ta zumunci,haka ta shiga wasan buya da gidan auranta,gidan da akan idanunta aka qage shi don cikar farin cikin ta. A qarshe ya juye ga cikamakin cikar baqin cikinta,a hakan dai har aka qare bikin Samira. Fuskarshi a sake,ya dubi mahaifiyarsa."Ya ne na ganki haka hajiya? An yi biki an qare lafiya mai kuma ya saura?" Ta dube shi da bacin rai kamr ba ta yi magana ba,ta daure tace" a duniya wane aba muka yi wa Ummukalsum har ta ke qymatar zuri'ar, Ummukalsum har take kyamatar zuri ar yan uwa na Abdulrashid? Ban fahimtaba hajiya , me kuma ya biyo bayane ? Me kuwa bai biyo bayaba ? kasan cewar ka zama solobiyo , ka kasa tsinkayar tozarcin da matarka tayi mana ance ta kauracewa gidan tun farawar bikin samira ta kulle ta garkame duk wani abu da ke kasan gidan, sabida gadaruwar mallakinta ne , ko kuwa menene? Yarinyar nan Hanan ta shiga kai komon ababan da za a rufa asiri a cikin aljihunta , kasancewar kai kayi nisa baka nan , yar mulkin kuma ta garkame duk wani abu na amfani da ta kwan da sanin za a amfana dashi , ta kuma fice abinta , sabida tana kyamatar yan uwanka kasancewar ta fito daga tsatso na alkalami da takarda? Ta gyada kai cike da jimami Babu ko shakka yarinyar nan tana nufin kunyatani , amma da yake Allah yafita sai shi ya mana katari da matar kirki , matar karamci , matar da abin hannunta ma sam ba a gabanta yakeba balle abin da yake karkashin ikon miji , hakan kuma ya nunar min lallai ana kwarar yarinyar nan. ita da keda iyali ai yakamata ragamar komai ya zamo a hannunta. Yayi shiru yana sauraran mahaifiyarshi , zuciyar nan tashi sai tafarfasa take , takamar sunyi arziki tare ai bai zamo cewa ita ta fita ta nema mishiba aah jibi da guminshi ne ya tara mishi , balle ta nemi zame mishi karfen kafa , ba sididi ba sadada , balle ace gudan jini ya gilma a tsakaninsu (da) a kauda kai domin albatkacinsa. Kiyi hakuri hajiya zanyi wani abu a kai, kinsan dai lallai bansan wannan tozarci na Ummukalsum ba. Oh inma ka sani ka sani mai zaka iya rashidu? kasancewar an wanke an shanyeka matarka na yadda take so nidin nan ban isa duban kirki a idanuntaba ? babu ko shakka yarinyar nan ta bata wayonta , da ina dubanta yarinyar kirki. Tana haramar kwanciya bacci ta jiyo motsin kikam a tsaye a kanta yanai mata wani duban lalaci. Banyi mamaki ba kasancewar wanda bai daraja tsoffinsaba yaushe ko zai girmama tsoffin wasu ? saidai wai hakan ba yana nufin zan saka idanu ga cin zarafin tsoffina ba , bana taba ja da al amuransu balle har in zamo mai kunnan kashi ga muradinsu. hakan tasa na zamo cikin albarka da yalwa da arziki da wadata. Ta rasa da wace sigar zata wassafo lamari , nan take kwanyarta ta dau caji abin haushi ta rasa tsikayo abin kirki , meye musabbabin wannan cin zarafi da Abdulrashid yayi mata? a iya tsinakayenta suna zaman lafiya da surkarta da dadi ba dadi dai a hakan suke hakuri da junansu musamman tin bayan faruwar al amura da yawa. Yadda zatin surarshi ya russuna haka sautin muryarshi ta russuna a gaban professor nuhu, cikin shiryayyen kalamai ya tsarance professor da miyagun ta adun diyarshi da yake matukar hakuri da halinta , lamarin har ya kai gangara ga tsoffinsa. Ran professor yakai makura wajen daci , Kayi hakuri Abdulrashid, kaci gaba da hakuri da halin Ummukalsum babu ko shakka yarinta ke dibanta , har yanzu nan ta kasa sanin ciwon kanta , yaushene Ummukalsum za tayi hankaline? Ya tuhumi kansa cike da tarin jimami. Zanja kunnanta zanyi hukunci na karshe a kan Ummukalsum, ka saka idanu ka gani. Baiso dai hakanba , yasone professor yakai ga furucin Idan baka iya jurewa halin diyata ka sakota ko zukantanku sa huta ga miyagun ta adun Ummukalsum. Shikenan da hakan ya fiye masa , da ba akai ga yi mishi zargin kasa maida halacci ba, harma akai ga yi mishi tuhumar butulci.

1 comment:

  1. Ngomong apa ente sakamakon alkairi ano tak paham betul jo

    ReplyDelete

Powered by Blogger.