Header Ads

Hakikanin kaunar Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama.( Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

Alhamdu lillahi rabbil A’lamin, Wa sallallahu wa sallama ala Nabiyyina Muhammad wa ala alihi wa sahbihi ajma’in. Amma ba’ad; Lallai wanda yake son Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama zai fifita shi akan duk abin da yake da girma ko daraja ko tsada a gunsa. Domin son Allah da manzonsa sune imani, kuma imanin bawa bazai cika ba sai da su. Allah subhanahu wa ta’ala yace: “ kace idan har iyayenku da ‘ya’yanku da ‘yan uwanku da matanku da danginku da dukiyar da kuka tsuwurwurta da kasuwancin da kuke jin tsoron tasgaronsa da gidaje da kuke yarda dasu sune suka fi soyuwa a gareku daga Allah da Manzonsa da jihadi saboda Allah ;to ku zauna har Allah ya zo da al’amarinsa, allah baya shiryar da fasikai” {Tauba :24} Wannan ayar nassi ce karara a bisa wajibcin kaunar Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama,da wajibcin gabatar da wannan kaunar akan duk wani abin kauna. Alkali Iyadh yace: “wannan ayar ta isa wajen zaburarwa da fadakarwa da shiryarwa da zama hujja ta gaske a bisa wajibcin kaunar Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama da cancantarsa da wannan soyayyar, domin Allah ya kwankwashi wadanda dukiyarsu da iyalansu da ‘ya ‘yansu suka fi soyuwa a garesu fiye da Allah da manzonsa,kuma yayi musu narko cewa su jira har Allah ya zo da al’amarinsa,sannan ya fasikantar da su, ya kuma sanar da su cewa sun bacewa hanya madaidaiciya, Allah ba zai shiryar da su ba. Hakanan kuma wanda ya yi la’akari da wannan ayar zai ga cewa umarnin bai tsaya ga samuwar soyayya ga Allah da Manzonsa kadai ba, barima dai dole ne sai wannan son ya zama sama da son duk wani abu wanda ba su ba. Wa sallallahu wa sallama ala Nabiyyina Muhammad wa ala alihi wa sahbihi ajma’in.

No comments

Powered by Blogger.