Header Ads

Mas’alolin aure Fitowa ta 23(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

TAMBAYA Wace addu`a ya kamata a yi wa Ango da Amarya? AMSA: Addu`ar da ake yi musu ita ce: ﺑﺎﺭﻙ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻚ ﻭﺑﺎﺭﻙ ﻋﻠﻴﻚ ﻭﺟﻤﻊ ﺑﻴﻨﻜﻤﺎ ﻓﻲ ﺧﻴﺮ . Ma`ana: Allah ya sanya maka albarka, kuma Allah ya sanya albarka a cikin aurenka, kuma ya hada tsakaninku da alheri. Wannan addu`ar tana daga cikin addu’o’in da suka tabbata daga bakin Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ga al’ummarsa idan sun yi aure. TAMBAYA: Yaya magabata na kwarai suke gabatar da bikin aurensu? AMSA: Magabata na kwarai sun kasance suna yin biki yadda shari’a ta yarda da shi. Yana daga cikin tsarin bikinsu, koyawa amarya yadda za ta yi ado da sanya lalle da dukkan kwalliyar da ta kamata. Domin kamar yadda ya gabata, Ummu Sulaim ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ta yi wa Nana Safiyyah ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ kwalliya ta mika ta ga Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ranar tarewarta. Sai dai a kiyayi yin ado da kaya masu shara-shara, wadanda suke bayyana al`aura ko dukkan kwalliyar da ta sabawa shari`a, kamar aske gashin gira, ko maza su yiwa mata kwalliya, da dai sauransu. Haka kuma yayin da mata suke kai amarya gidan mijinta, za su iyayin wakokin da suka dace, wadanda ba su sabawa shari`ar Musulunci ba. Kuma ya halatta a yi kidan da babu batsa a cikinsa, kamar kidan shantu ko na kwarya da sauransu. Domin hadisi ya tabbata cewa: Nana A’isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ da sauran mata sun kai amaryar daya daga cikin mutanen Madina. Sai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya tambaye ta cewa: … ﻳﺎ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﻣﺎ ﻛﺎﻥ ﻣﻌﻜﻢ ﻟﻬﻮ ؟ ﻓﺈﻥ ﺍﻷﻧﺼﺎﺭ ﻳﻌﺠﺒﻬﻢ ﺍﻟﻠﻬﻮ . Ma’ana: Ya A’isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ wane irin nishadi/wakoki kuke yi yayin kai amaryar? Domin hakika mutanen Madina sun kasance masu son nishadi/wakoki ne. Haka kuma a nisanci cakuduwa tsakanin maza da mata yayin biki, sannan a guji yin koyi da Kiristoci wurin kai amarya, kamar sanyawa amarya doguwar riga fara irin ta Coci, da yi wa motar kai amarya ado da fulawoyi ko balo-balo da sanya wa amarya ko ango zobe da yanka kek da tafiya bakin ruwa (picnic) da yin rawa tsakanin maza da mata wasu ma har suna lika kudi da sauransu. Kuma bai halatta ba a rika daukar hotunan mata, musamman matan aure a kyamara ko hoton bidiyo, wanda yawanci suke caba ado tare da bayyana tsiraici, wani lokaci ma suna rawa a irin wannan hali marar kyan gani, kuma wasu mutanen da ba muharramansu ba suna kallon wadannan hotunan. Wannan yana nuna rashin kishin wasu mazaje. Kuma a karshe yana sabbaba bala`i na neman matan mutane da dukkan nau`ika na alfasha. Dukkan wadannan abubuwan da muka lissafa sabawa Allah ne da Manzonsa sallallahu alaihi wa sallama. Don haka wajibi ne a matsayinmu na Musulmi mu nisanci dukkan nau’in maguzancin Turawa da Kiristoci a wurin bukukuwanmu. Babban abin takaici shi ne irin yadda ake yi ranar kai amarya, amare da angwaye suke shagala ga barin salla, musamman Sallar Magariba da Isha`i da Asuba. Wannan kuma babban laifi ne, don bai kamata ba a ce ranar da amarya za ta sanya kafa dakin mijinta, ta kasance ta sabawa Allah da Manzonsa sallallahu alaihi wa sallama. Haka kuma al`adar nan ta sayen baki, ita ma ta sabawa koyarwar Addinin Musulunci, saboda cakuduwar da ake yi tsakanin abokan ango da kawayen amarya wadanda ba muharramansu ba, da kuma abubuwan da suke yi wadanda ba su halatta ba. A karshe ya kamata a fahimci cewa, dukkan al`adar da ta sabawa Shari`ar Musulunci ba abar yi ba ce. Don haka a nisance ta, domin samun albarka da zuriya ta gari da rabauta daga Allah Madaukakin Sarki. Bayan duk abubuwan da muka yi bayani a baya, akwai wasu bukukuwa da aka aro daga Turawa, kamar bikin cika shekarar aure (ana yanka kek), ko bikin cikar shekarar haihuwa da makamantansu. Duk wadannan kwaikwayo da Yahudu da Nasara ne, bayan kuma Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya umarce mu da mu saba musu a cikin ayyukanmu. TAMBAYA: Mene ne hukuncin saka hoton ango da amarya a kalanda ko kati tare da ayoyin Alqur`ani ko hadisan Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama a rarrabawa mutane? AMSA: Yin wadannan sabawa Shari`ar Allah ne karara, da wulakanta ayoyin Alkurani da hadisan Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama, da kuma jahiltar addinin Musulunci tare da sabawa kyawawan al`adunmu na gari da muka gada. Kuma wani babban abin bakin ciki ma shi ne yadda za ka ga irin wadannan hotunan masu dauke da sunan Allah ko hadisan Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama an zubar da su a bola (juji) ko kuma wurin kazanta bayan an gama bikin . Wannan yana nuna irin rashin kishin wasu mutanenmu, ta yadda za ka ga an buga hoton ango da amarya ta yi ado cikin gwalagwalai da kaya masu bayyana siffar jikinta. Tare da haka, wasu ma har lambar wayarsu suke sanyawa a jikin hoton wanda wannan zai iya ba da kofar wata fitina ta samu. Da fatan Allah ya shirye mu baki daya.

No comments

Powered by Blogger.