Header Ads

Mas’alolin aure Fitowa ta 24(Sheikh Abdulwahhab Abdullah)

TAMBAYA: Me Sunnah ta tanadarwa ma’aurata a ranar tarewa? AMSA: Abubuwan da sunnah ta kwadaitar da ma’aurata a ranar tarewa suna da yawa, amma za mu kawo kadan daga ciknsu. 1- Da farko, ana so ango ya karbi amarya da tausasawa, saboda kasancewarta bakuwa a wannan ranar. Sannan a ba ta wani abin sha kamar nono ko madara. Domin hadisi ya tabbata daga Asma’u bint Yazid ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ cewa: ranar da aka kai wa Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama Nana A’isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ya ba ta nono ta sha. Kamar yadda muka bayyana a baya. 2- Kuma ana so ango da amarya su yi sallah raka’a biyu tare a wannan daren. Kamar yadda ya tabbata daga Abi Wa’I’ll ya ce: ﺟﺎﺀ ﺭﺟﻞ ﻣﻦ ﺑﺠﻴﻠﺔ ﺇﻟﻰ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﻘﺎﻝ ﺇﻧﻲ ﻗﺪ ﺗﺰﻭﺟﺖ ﺟﺎﺭﻳﺔ ﺑﻜﺮﺍ ﻭﺇﻧﻲ ﻗﺪ ﺧﺸﻴﺖ ﺃﻥ ﺗﻔﺮﻛﻨﻲ ﻓﻘﺎﻝ ﻋﺒﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﺇﻥ ﺍﻹﻟﻒ ﻣﻦ ﺍﻟﻠﻪ ﻭﺇﻥ ﺍﻟﻔﺮﻙ ﻣﻦ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ ﻟﻴﻜﺮﻩ ﺇﻟﻴﻪ ﻣﺎ ﺃﺣﻞ ﺍﻟﻠﻪ ﻓﺈﺫﺍ ﺃﺩﺧﻠﺖ ﻋﻠﻴﻚ ﻓﻤﺮﻫﺎ ﻓﻠﺘﺼﻞ ﺧﻠﻔﻚ ﺭﻛﻌﺘﻴﻦ … Ma’ana: Wani mutum ya zo wurin Abdullahi (Ibn Mas’ud radhiyallahu anhu) sai ya ce masa: hakika na auri yarinya budurwa, amma ina jin tsoron kada mu rabu. Sai Abdullahi Ibn Mas’ud radhiyallahu anhu ya ce da shi: Kauna da soyayya daga Allah ne, sabawa da fitintinu kuma daga Shaidan ne. Don haka ranar tarewar ku, ka umurce ta ku yi sallah raka’a biyu tare, ita ta tsaya a bayanka … 3- Kuma an so ango ya dora hannunsa a kan makwarkwadar amaryarsa sannan ya roki Allah da addu’ar da ta tabbata daga Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam, inda ya ce: ﺇﺫﺍ ﺗﺰﻭﺝ ﺃﺣﺪﻛﻢ ﺍﻣﺮﺃﺓ ﺃﻭ ﺍﺷﺘﺮﻯ ﺧﺎﺩﻣﺎ ﻓﻠﻴﻘﻞ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺇﻧﻲ ﺃﺳﺄﻟﻚ ﺧﻴﺮﻫﺎ ﻭﺧﻴﺮ ﻣﺎ ﺟﺒﻠﺘﻬﺎ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺃﻋﻮﺫ ﺑﻚ ﻣﻦ ﺷﺮﻫﺎ ﻭﺷﺮ ﻣﺎ ﺟﺒﻠﺘﻬﺎ ﻋﻠﻴﻪ . Ma’ana: Idan dayanku ya auri mace ko ya sayi mai yi masa hidima, to, (ya kama makwarkwadar kanta/sa), sannan ya ce: Ya Allah ina rokonKa dukkan alherin da yake tattare da ita da dukkan alherin da aka dabi’antar da ita a kan shi, kuma ina neman tsari a gare ka daga dukkan sharrin da yake tattare da ita da dukkun sharrin da aka dabi’antar da ita a kai . 4- Kuma yana daga cikin abin da ake so ranar tarewa da sauran ranaku a yi addu’a yayin saduwa kamar haka: ﺑﺴﻢ ﺍﻟﻠﻪ ﺍﻟﻠﻬﻢ ﺟﻨﺒﻨﺎ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ ﻭﺟﻨﺐ ﺍﻟﺸﻴﻄﺎﻥ ﻣﺎ ﺭﺯﻗﺘﻨﺎ . Ma’ana Bismillahi, ya Allah ka nesantar da mu daga Shaidan kuma ka nesantar da Shaidan daga abin da za ka azurtamu da shi (na ‘ya‘ya). 5- An fi so kafin mutum ya kusanci iyalinsa su yi asuwaki, domin yin asuwaki sunnar Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam ne. Kuma hadisi ya tabbata daga Mikdam Ibn Shuraih daga Babansa radhiyallahu anhu ya ce: ﺳﺄﻟﺖ ﻋﺎﺋﺸﺔ ﻗﻠﺖ ﺑﺄﻯ ﺷﻰﺀ ﻛﺎﻥ ﻳﺒﺪﺃ ﺍﻟﻨﺒﻰ -ﺻﻠﻰ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻠﻴﻪ ﻭﺳﻠﻢ - ﺇﺫﺍ ﺩﺧﻞ ﺑﻴﺘﻪ ﻗﺎﻟﺖ ﺑﺎﻟﺴﻮﺍﻙ . Ma’ana: Na tambayi Nana A’isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ cewa: Da mene ne Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallam yake farawa idan ya shigo gidansa? Sai ta ce: Yana fara wa da yin asuwaki. 6- Kuma an fi so ango da amarya su kasance cikin tsafta wato su nisanci kazanta tare da sanya turare. Haka kuma shari’a ta halatta wa mutum ya sadu da iyalinsa ta yadda yake so. Amma ban da dubura ko kuma yayin da take yin jinin haila ko biki. A nan muke nasiha ga mutanen da suka jarrabtu da saduwa da iyalinsu ta dubura, ko yayin da suke jinin haila ko biki, da su nisanci wannan mummunar dabi`a, domin babban sabon Allah ne. Kuma bai halatta ba matan su yi musu da`a ko da kuwa hakan zai kai ga rabuwar aurensu. Amma babu laifi a Shari`ance ma`aurata su kalli al’aurar junan su ba tare da wani shamaki ba, domin hadisan da ake fada cewa, wai Nana A’isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ta ce: tunda take ba ta taba ganin al`aurar Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ba, shi ma kuma bai taba ganin ta ta ba, wannan kage ne aka yi wa Nana A’isha ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ . Haka kuma akwai wani littafi da ake kira ‘Kurratul Uyun’ wanda a cikinsa ne ake tattaro irin wadannan hadisan da ba su tabbata ba, mafi yawansu ma kage ne aka yi wa Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama. Sannan kuma akwai wani littafi da ake kira ‘Wasiyyar Annabi sallallahu alaihi wa sallama ga Sayyadina Ali radhiyallahu anhu’ a cikin littafin ana cewa wai Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya cewa Sayyadina Ali radhiyallahu kada ka sadu da matarka a sararin da zaka ga farin wata ko tauraruwa ko kuma kada ka sadu da ita face sai ku na lullube da mayafi. Duk wannan kage ne aka yi wa Annabi sallallahu alaihi wa sallama da Sayyadina Ali radhiyallahu anhu, wannan bai inganta ba a wurin malaman hadisi. 7- Shari`a ta hana mace ta ki bayar da kanta yayin da mijinta ya nemi ya yi sunna da ita, haka shi ma mijin yayin da matarsa take nemansa bai kamata ya ki sauraronta ba, ba tare da wani uzuri ba. Domin hadisi ya tabbata daga Abu Huraira radhiyallahu anhu ya ce: Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya ce: ﺇﺫﺍ ﺩﻋﺎ ﺍﻟﺮﺟﻞ ﺍﻣﺮﺃﺗﻪ ﺇﻟﻰ ﻓﺮﺍﺷﻪ ﻓﺄﺑﺖ ﺃﻥ ﺗﺠﻲﺀ ﻟﻌﻨﺘﻬﺎ ﺍﻟﻤﻼﺋﻜﺔ ﺣﺘﻰ ﺗﺼﺒﺢ Ma’ana: Idan mutum ya kira matarsa zuwa shimfidarsa sai ta ki, to, Mala`iku za su rika tsine mata har sai gari ya waye. 8- Haka kuma Shari`a ta hana ma`aurata su rika fallasa asirin junansu a wurin kawaye ko abokai. Misali su rika fadin yadda suke saduwa da juna da dai sauran al`amura na sirri da suke gudana a tsakaninsu. Domin hadisi ya tabbata Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama yana cewa: « ﺇﻥ ﻣﻦ ﺃﺷﺮ ﺍﻟﻨﺎﺱ ﻋﻨﺪ ﺍﻟﻠﻪ ﻣﻨﺰﻟﺔ ﻳﻮﻡ ﺍﻟﻘﻴﺎﻣﺔ ﺍﻟﺮﺟﻞ ﻳﻔﻀﻰ ﺇﻟﻰ ﺍﻣﺮﺃﺗﻪ ﻭﺗﻔﻀﻰ ﺇﻟﻴﻪ ﺛﻢ ﻳﻨﺸﺮ ﺳﺮﻫﺎ ». Ma’ana: Hakika yana daga cikin mafi sharrin mutane a wurin Allah ranar tashin alkiyama, mutumin da ya samu sakewa da matarsa, ko kuma matar ta sake da shi yayin saduwa, sai ya zo yana bada labari, ko ita ta je tana ba da labari. Amma babu laifi ma’aurata su bayyana abubuwan da suka dace a shari’a, musanman hukunce- hukuncen fikihu, da koyar da rayuwar aure a shari`ance, kamar yadda matan Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama suka rika gayawa sauran mata yadda suke wanka tare da shi, da sauran abubuwan da suka shafi zamantakewarsu ta aure, wannan ya tabbata a cikin hadisai da da ma. FADAKARWA Yana daga cikin sunnar magabata, kyautatawa ango da amarya ta hanyar ba su kyaututtuka na abinci da sauran abubuwan amfani na yau da gobe a cikin kwanakin angwancinsu da bayan tarewarsu, sai dai kada su kallafawa kansu abin da ba za su iya ba. Domin hadisi ya tabbata daga Anas Ibn Malik radhiyallahu anhu ya ce: ﻟﻤﺎ ﺗﺰﻭﺝ ﺍﻟﻨﺎﺑﻰ ﺯﻳﻦ ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ﺃﻫﺪﺕ ﻟﻪ ﺃﻡ ﺳﻠﻴﻢ ﺣﻴﺴﺎ … Ma’ana: Yayin da Manzon Allah sallallahu alaihi wa sallama ya auri Nana Zainab ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ , sai Nana Ummu Sulaim ﺭﺿﻲ ﺍﻟﻠﻪ ﻋﻨﻬﺎ ta aika masa da kyautar abincin da ake kira Haisan (wanda ya kunshi dabino da cikwi da kuma mai a hade)… Haka kuma yana daga cikin sunnah a taya ango da amarya murnar bikinsu tare da yi musu addu`ar neman zaman lafiya kamar yadda muka yi bayani a baya. Ma’ana mutum ya ce da su: ﺑﺎﺭﻙ ﺍﻟﻠﻪ ﻟﻚ ﻭﺑﺎﺭﻙ ﻋﻠﻴﻚ ﻭﺟﻤﻊ ﺑﻴﻨﻜﻤﺎ ﻓﻲ ﺧﻴﺮ

No comments

Powered by Blogger.