YAUCE RANAR MATA TA DUNIYA
YAU RANAR MATA NA DUNIYA *SU WAYE......MATA*? Kalmar MACE tamkar (GOLD) ne ko kuma muce Sinadarin ZINARI mai yin WALKIYA a kowane LOKACI, MATA, Sunada wani SINADARI na Farin JiNi wanda yake da matukar Tasiri idon MAZAJE, MATA, Sunada matukar kima a Cikin Al'Ummah wadda har takai ga sun samu martaba da matsayi Babbah, MATA, Sunada wani LAUNI mai Juya MAZAJE, Tamkar Limzamin DOKI har ya kai ga komai MATSAYINKA, MULKI, KUDI ko SARAUTA. MACE sai ta Juya ka, MATA, Sun Amsa Sunan Su MATA ga jan AJI da Juyin Juya Hali, komai Rashin Kyan MACE Kalma daya Zata sa KASO ta nan Take, MATA, Sunada Hikima da Jurewa akan abunda suke matukar SO, amman sai sukasa Nunawa, MATA, Sunada Kunya, Hakuri da Juriya har sukan burgeka idan Ka Iya Zama Dasu, MATA, Basu son mai kuntata masu koda yaushe sunfi son Mai kyauta ta masu, MATA, Suna son RAHA da Abun DARIYA ko kuma Nishadantarwa, MATA, Zuciyar su FARA ce tamkar farin RUWA ba wuya shawo kansu idan ransu ya Baci, MATA, Sunada HAKURI da Tausayi da kuma Firgita akan wani abu Kadan, MATA, Basa son, Saunan Mutum ko kuma Qazamin Mutum, MATA, Sunfi son mai BASU ako wane Lokaci da kuma nuna Tausayi agare SU. MATA, Suna jajir cewa akan nuna SOYAYYA da Tausayin Junan SU, MATA, Sunfi son mutum mai HAKURI da zafin naima har sukan yin Alfahari da Wannan, ~MATA, Sunada Yauqi da son DAULA da kuma Anunasu Manya ne, DARAJOJIN MATA GUDA (16) DA SUKA DARA MAZA! (UUSIKUM FIN NISA'I KAIRA) Inai muku wasicci da Alkairi ga mata "Inji Manzon Allah {s.a.w} a cikin Hudubar Ban Kwana" 1- MACE CE, TA FARA MUSULUNTA a duk duniya kuma ta yiwa musulunci hidima da dukiyar ta da duk abinda ta mallaka harda GwalaGwalanta (NANA KHADIJA) (R.A) 2- MACE CE, Farkon wanda ta fara Istimbabi a cikin shari'ar musulunci........ (NANA KHADIJA) (R.A) 3- MACE CE, Sanadiyyar samun Taimama a shari'a (UMMUNA A'ISHA) R.A 4- MACE CE, Ta ilmantar da Sahabbai bayan wafatin Annabi{s.a.w} NANA A'ISHA (R.a) 5- MACE CE, Sanadiyar tsiran sahabbai daga fushin Allah sanda akai sulhun HUDAIBIYYA Kuma MACE ce ta shawo akan SAHABBAI har suka tsira daga fushin Allah. (UMMU SALAMA) R.A 6- MACE CE, Ta Kwantarwa Manzon Allah HANKALI Lokacin da Ifk ya faru a madina, kafin saukar wahayi (BARIRA) (R.A) 7-MACE CE, Wanda Manzon Allah {S.A.W} yace idan mutum ya tarbiyyantar da ita koda bashi ya haife ta ba, zai shiga ALJANNA shi da Manzon Allah {S.A.W} 8- MACE CE, Ta zamo Ma'auni da mai Aure zai gwada kimarsa agun Mahaliccinsa, idan ya kyautata mata yanada sakamako mai kyau, idan kuma ya cuceta akwai uquba daga Allah. 9- MACE CE, Shari'a ta tanadar MATA Ladan Jam'im Salloli guda biyar (5) Da Juma'a da Jana'iza da Jihadi duk basai taje ba,amma sanadiyyar ta Kyautatawa MIJINTA Allah Zai bata duk LADAN wadannan Ibadun. 10- MACE CE, Sanadiyyar warware matsalar Zihari, suratul(MUJADALA) 11- MACE CE, A duk qur'ani ba sura mai sunan maza sai mata Suratul (NISA'I) 12- MACE CE, Ta fara yin Sa'ayi tsakanin SAFA da MARWA (HAJARA) 13- MACE CE, Sanadiyyar tsiran mutanen sarauniyar Saba, suratl(NAML) BILKISU MAI GADON ZINARI 14- MACE CE, Sanadiyar musuluntar Sayyiduna Umar (R.A) (FATIMA) 15- MACE CE, Ake samun nutsuwa da ita! LITASKUNU ILAIHA, Namiji bazai taba samun sukuni ba sai yana da mace! 16- MACE CE, Duk mulkin mutum da dukiyar shi sai da ita yake kara kima a idon mutane! godiya nake.
Mun gode
ReplyDelete