Header Ads

*MIJIN KADDARA part4***

iya bata ce uffan ba tafi..ahaka na wuni zuciyata fal bakin ciki kaina na saramin ko abinci ban iya ciba sai da magriba bayan nayi wanka nasa doguwar riga burbery mai kwalliya awuya naji yunwa na neman min illah na dafa indomie da kyar naci ina falo sadik ya dawo ya wuceni ba sallama na bishi room na sameshi akwance agado na tsaya akansa ina huci bai kalleni ba cikin kuka nace nayi takaici babba dana aureka amatsayin MIJIN KADDARA sai yanzu nayi tunani badan allah kake sona ba kaso nine domin kyan halittata da kyauna da kuma shawa'ata data debeka wlh ka cuceni ka rabani da masoyina mansur kasa naci amanarsa..sai kuka sadik ya mike zumbur yace mayaudariya meye ban muku ba arayuwa wawiya da kika zalinci dake da sakaran iyayenki akan kudi ni kuma dan sha'awa na aureki ko yanzu kudi yayi magani domin na biya bukatata. . na kalleshi arazane nace wlh ni kuma bani ba zubar da ciki sai dai ka kasheni..sadik yace dole ki zubar azzaluma mayaudariya..cikin karajin kuka da magana da karfi nace ya isheka sadik!!ka dade kana kirana da azzaluma mayaudariya kada ka kara fadamin domin kaine mayaudari kuma banga abinda nai maka ba a auranmu..sadik afusace yace kinmini shin ina kwayoyin da nake baki in zamu kwanta kullum tabbas da kinasha da baki dauki juuna biyu ba domin da tuni ya lalata miki mahaifa..asanyaye nace allah ya tuni asirinka ashe wannan ce nufinka ka cuceni to ban shaba allah na godema..sadik yaxe ya muke ciki dake kin zabi saki akan azubar da ciki dominni ban aureki bane domin haihuwa ba sai domin dadin rayuwata..ina hwy na fara tunani bansan sanda nace shikenan na yadda acire cikin..sadik yace ki shirya gobe muje asibiti..ya kuma gado abinsa yaja bargo nafi minti talatin ina kas ina kuka sannan na fice... . Da safe tuni mun shirya jikina ba kwari ga tsoro ko kwalliya banyi ba saboda fargaba amotarsa muka iso asibitin abokinsa kalid aka wuce dani tiyata room ina tsaye jikina na rawa kalid ya mikomin wasu kwayoyi yace insha sannan ga gado in kwanta zan fita daga hayyacina sannan sui aikin cire cikin..na amsa nace doctor shin zan mutu yayin cirewar..kalid yace no ki dena sa wannan aranki mutuwa sai allah yayi kisha mana. . bansan lkc dana watsamai maganin afuska ba nace ashe kaima munafukine baka kaunata anayin likita domin samun lada ashe kai kwararren daukar rayuwakan bayin allah ne tun basu zo.. . tana gama fadar haka ta fito da sauri daga dakin tiyatar..sadik na zaune akujera yaga zeenat ta fito ranta abace zumbur ya mike yace zeenat ya kika fito lafia..zeenat ta gallah mata harara tai wani tsaki ta fice daga asibitin sadik ya dinga kwala mata kira amma ko waigenshi batai ba..alkc doctor kalid ya fito agigice ya nufu sadik..zeenat tafiya tai tayi har bakin titi cikin sauri ta tare keke napep tahau..tana isa gida bedroom ta shige ta zauna ta rushe da kukan bakin cikin wannan auran dabai kareta da komai ba sai kaddara..alkc sadik ya shigo da sauri ya akan zeenat yana huci da gumi cikin kakkausar murya yace kin kyauta da kika kunyata agaban mutane kuma wlh sakamako na daf sauka akanka. . zumbur zeenat ta mike tace na gwammace in kunyata akan in sabi mahaliccina wlh ko kadan bazan baku damar hadinkai dakai da dotor ba wajen aiwatar da kisa alhalin ba abunda ya muku hasalima baizo duniyar ba sai dai kamin kuma menene..sadik ya zare jajayen idanunsa yace tabbas banga amfanin zama dake arayuwata ba na sake ki saki uku kuma bani bake sannan kije ki rike dan cikinki inkin haifa kada ki nufushi dashi..ya juya ko kallona bai ba ya wuce abinsa na kama kuka amma ta wani bangaren sai naji sakin yafi akan wannan bakin zaman na tattara kayana akwati na fito afalo na sameshi yana kan kushin yana kallan ball a t.v nai kamar zan huceshi na tsaya nace azzalumi! mayaudari!!macu ci!!!wlh ka cuceni amma akwai ranar kin dillanci insha allahu za'ai walkiya kuma za'a ganka karshenka dana sani gami da nadama..sai kuka ya kwace mata tai gaba sadik yace hmmm kwadayi kenan dama duk wata yahau motar kwadayi sai ta saukeshi atashar wulakanci abinda kika shuka ne na ha'intar mansur..na kuma gida iya abu taita kuka ga malam jikinshi ya matsa watana biyu agida allah yayiwa malam rasuwa munsha kuka ga talauci ga maraici dame zamu ji..iya abu tuwon siyarwa ta kama yi akasuwa da daddare tai kosai dashi muke samun rufin asiri ni kowa alokacin ciki ya tsofa wata takwas gashi alayinmu an fara gulmata wasu suce naki zaman aure wasu suce dama kwadayine..cikina wata tara ya zamana tashi da kyar nake yi zainab kawata tazo ina ganinta sai kuka na kama tambayar ina mansur yana gidan mahaukatan ko ya mutu..zainab tace wlh ban sani ba..

No comments

Powered by Blogger.