Header Ads

SANADIN BOKO 2-01

Duk gidan da na shiga kalmar iri daya ce,wato baya shigowa. da hanxari na nufi gidan su maman rahma,ita bata nan ma sai matar wansu tace min shadad bai xo ba, na dawogida na sake duba ko'ina, rijiya a datse da kwado, don haka ban kawo xaton ya fada ba. na dubi takalman shi da takardun makarantarshi da yake hm work, sai naji kuka ya kufce min. nayi-nayi,sannan na mike na sake fitowa, wata daga cikin makotana ta same ni tsaye kofar gida ina ta leke-leke,tace "kin ko gan shi? nace,"a'a." cikin muryar kuka tace "ikon Allah, to ke ina ki ka tafi ki ka bar shi? nace,bakin kasuwa naje, kuma nakan bar fa. tace da kin sani nan gidanmu ki ke turo shi in xa ki fita.kila fakonki aka yi kina fita aka xo aka dauke shi, na tsura mata ido. su wanene xa su dauke shi? tace, oho.mugu yana nuna kanshi? aka dauki babba ma bare yaro, ke dai wannan rayuwa tamu ba sai dai addu'a ba. nace,to su wanene xa su fake ni?ban jira amsa ba na juya cikin gidan,tamkar mai shirin daukan wani mataki.tace,kije ofishi 'yan sanda ki kai rahoto,ban juyo ba kuma ban tanka ba, a tsakar daki na zauna gwaraf,idanuna suna ta kai kawo guraran yin 'yan tsalle-tsallen shi, naji na fashe da kuka. hakika wadanda suka daukar min yaron nan ba su min adalci ba, don bani da wanda ya fishi duk fadin kano, naci kukana ma ishi, bani da mai bani hakuri, na share hawaye. abu tamkar wasa, sai gashi har anyi kiran sallar azahar,jikina a mace nayi sallah,ina zaune ina addu'a hawaye na bin kumatuna, sai naji sallamar maman su rahma,na amsa ba tare da na share hawayan ba. ta shigo tana cewa, hafsa kin ko ga maigidan nawa? sabon kuka ya kufce min, cikin muryar mai kuka nace wallahi har yanxun mama, tace na dawo kawai sai suke fada min wai kun xo neman shadad,hankakinki tashe. na ko ro mata wajibin duk abubuwan da suka faru, zama tayi rike da baki tana salati, tace lai finki ne in gidan mu yayi nisa ki rike hannun abunki kije dashi mana, angaya maki yanzu kaza batafi dan adam ba ne? Wlh sai kaza ko rago yayi yawanshi han kali kwace amma bil adam yana tafe ana cinikinsa, na sake fashewa da kuka, nace mama tunfa bai kai haka ba ina barinshi a gida, tace to yanxu me zaki fadawa dangin uban shi da iyayenki? Na mai maita kalmar dangin ibanshi? A cikin raina. Sallamar shi ne cikin murna ta ka tseni, anty na yau mun sha yawo da uncle dina, ya fado jikina, munje gurin wasa na hau doki da duniyar sama, mun sha ice cream, harma muka dau hoto. Ban bari ya sake cewa wani abuba na dagoshi na watsa mai wani irin mahaukacin mari, ya yanke da wani ihu sai ganin uncle din nashi mukayi a sukwane ya fado cikin gidan. Na han kadar dashi ya fadi na bishi da duka maman rahama tana a a-a a, ban tsaya ba ina dukanshi ina kuka. Shi kuwa uncle din nashi yana tsaye. Mama cikin jin haushi ta wanka min mari, tace ke ma haukaciyar ina ce? Za ki rufe dan wanan yaro da duka? Na dubeta ina kuka, mama wanan yaron yana jefani cikin damuwa, uban wanene yace yafita ba nanan saboda ya raina ni? Uncle din shi ya sa hannu ya dauke shi, yasa a kafada yana lalashi, shi kuwa sai tsala kuka yake. Cikin daurewar fuska yace, nasan haka zata faru, shi yasa ma na daukeshi ki san cewa kina kasada, ina sone kiji halin da zaki shiga in wani yai gaba dashi saka makon kasadar ki. Ya dubi maman rahama yace, mama don Allah ba kasada bane tatafi ta bar yaro shi daya, mai zai sa ba zata tafi dashi ba? Mamar rahama tace sakarya, nima yanzu na gama yimata fada, gwara da ka gwada mata hakan. Ni ko cikin takaici da masifa nace, ina ruwanka da shi? Menene hadinku da zaka zo ka dauke shi, shi shigi da kalata. Bai tankani ba, kilama bai fahimci hausar tawa ba. Mama tace jacan sakara, na shige daki bansani ba haushin daukar yaron nake ji ko farin cikin dawowarshi? Mama ina ji tana cewa kayi shuru. Kyale ta, kai kuma dana ka kyauta da kayi mata wanan ba razanar. Shi kuwa cikin hausarsu ta filani yola yake cewa, amma mama nikam banji dadin dukan nan da tayi mashi ba fa, da ma ni ta buga zanfi jin dadin hakan don nine na buga ya bude na tafi dashi. Na motsa ranta ne dan ta gane hakan na iya faruwa, in nace zan fada mata da baki bazata saurareni ba. Mama tace haka ne, ai hafsat shu‘uma ce, bayan yayi shuru, da kyar ya mikawa mama shi. Gashi mama, don Allah ki bata hakuri, na san cewa na taba ranta, amma fa kada ta sake dukan shi. Mama tace kada ka damu, gulmace ta sata dukanshi bakaga yanda ta haukace tana neman shi tana kuka ba. Yace Allah sarki! Ban san ko nawa ya ciro ba, naji dai yace mama ga wanan ki sai goro, sanan na jiyo murmushi yana cewa hafsat sai anjuma ko? Ban tamka ba mama ta shugo tana cewa, kinga harda kudi ya bani don Allah kiyi mashi godiya. Ta kwonto shadad a jikina, na turo baki nifa ban sanshi ba daga bikin rahama ya liki men. Wlh na rasa yanda zan yakice shi. Ta ce keko yarnan sai kace wace mujinta ya mutu da kurwarki? Nifa na tambayi rahama da lilin kin jama‘ar ki ta ke shai da mun tun rasuwar baban wanan yaro ne gashi kunyi zaman mutunci, to banda abinki hafsa itafa rayuwar duniya haka take kuma Allah ya fimu sanin abinda ya dace gare mu, don haka ki kula. Tan tahakiliki kila ya maye maki gurbin miji naki. Nace to na fada ne ba dan na amince ba sai don kada mama taga naki zancenta sanan ina son abar maganar cikin tarkace kayan zakin da ya sayowa shadad ne na ga hoton da suka dauka kala 3 sunyi kyau har wata zuciyar tace na yaga su sai kuma wata ta gargadeni da cewa mutumin nan bai cancaci haka a bayan idon sa ba. In kinyi masa a gaban idonsa yanzu sai ki mutunta hotonsa ko dan danki don haka sai na hakura na ajiye masa. Anfi saty banji duriyar shi ba hakan yayi min dadi shadad ne kanyi min zancen sa in na bala mashi harara sai yayi shuru don tun da na dakeshi yake dari dari da zancen uncle din sa. Nan na fahimci wani abu ga yaro shi yaro dan ja a jiki ne zagi duka baya gyara yaro janshi a jiki nuna mashi soyaya cusa mashi tsoron Allah yi mashi nasiha tare da bashi lbr magabata. Suna tai makawa gurin tarbiyya bana dukan shadad na fi yi masa duk abubuwan da na lisafa amma yau daya da na dukeshi duk ya shiga tai tayin sa. Kenan in baka yawan dukan yaro yafi tsoron dukan sannan ya fi jin magana. Wanan tunanin da nayi shiyaja na sake janshi a jiki, da dadare ya gama cin abinci yayi home work, nace ya bani lbr duk abinda ya faru a makarantar su. Nan zan tajin wane ya iya karatu wane ko an tada ya kasa, mun yi masa shem, nace kai fa ka kasa ko? Yace, ina yi anty, har antyn mu tace wai nine nafi kowa zan sake cin na 1 yanzu, nace to ka kara kokari har a islamiyya ka dage, yace uncle yace in na sake cin na 1 zai mun kyauta da ya so ko, uncle din shi sai na watsar da zancen. Nayi shuru ina tunanin yanda zanyi ga adashan da na kwasa gidan su maman rahama dubu 20 a hannuna kudin da naci burin inyi rigista da su, kuma ga kudin makarantar shadad, in ban da da ba cikin satyn nan zasu koro shi, kuma ni an kusa rufe rijista wata zuciya tace, tunda baki taba lattin biya ba kije ki nemi alfarmar suyi maki uziri, nan gaba sai ki basu. Don haka washegari naje naje nayi rigista ta, har kwana 4 ba sukori shadad ba, muna home work na ce wanan karon makarantar ku sunyi dagi amma gobe zanje in basu hakuri kada su koreka. Yayi caraf yace, anty an bani rasit wai na biya, ya tashi da gudu ya nufi ja karshi yana cewa, anty yau anyi kora ma, cikin mamaki na amshi rasit din ina dubawa, na shekara daya aka biya nace shadad wa ya biya maka kudin makaranta? Ya juya hannu tare da cewa ban sani ba. Da mamaki na kwana, da safe kuwa makarantarsu muka nufa kai tsaye bayan ya shiga aji ofishin mai karbar kudin makarantar, muka gaisa ta ganeni, nace shadad yazo da rasit wai an biya mashi kudin makaranta, wanda nasan ban kawo ba tace uncle dinshi bai fada maki zai biya ba? Na kasa magana, tace to shine ya zo ya biya na shekara 1. Sai sabuwar shekara zaki soma biya kudi. Da kyar na ce to shi kenan, na fita na nufi makaranta rai na a bace. Shi wanan habubakar din ba za ya fita hanyata ba kenan? Shi ma yana son dole sai ya cika burinsa a kai na. Tabdijan! Duk ranar da yasake gigin hada ido danine zan rufe idona ne in zage shi tas, yanda zai bar rayuwata ta huta. Abubakar lamido kyakyawan saurayi bafulatanin jahar adamawa dan yola, tuki yake cikin na tsuwa har ya isa gidansu tamgameme da ke bayan PZ, ya ajiye motar a mazaunin ta, sannan ya fito cikin takun na tsuwa ya nufi cikin gidan. Yan mata ne 2 a wadatacen palon duk kansu 1, sai dai in ka kali fuskarsu zaka gane daya tayi tsawon kafa ne, ta taras da yar uwarta. Suka amsa sallamarsa, karamar ta taso da sauri tana cewa (cikin harshen fillanci) sannu da dawowa hamma. Ya rumgumota gefen shi cikin harshen turanci ya ce mata. Yaya makaranta? Ta amsa da lafiya. Babar ta dubeshi da murmushi tare da mikewa tsaye dan girmama shi. Hamma sannu. Yace rukayya sannu da gida, ina dada tana ciki? Suka ce eh, tana ciki tare da baki. Ya nufi dakin shi, ummi tana rike da hahhun shi. Ya zauna bakin gado ya dubeta. Me kuka dafa? Tace tuwon semo da miyar kubewa danye. Je ki kawo mun shi kuma ya tube ya dan watsa ruwa ya tasa tuwon agabanshi amma ya kasa ci, tun lokacin da yaga hafsat ya ganeta daga muryarta duk da girman da tayi, bai sa ya kasa ganeta ba. Yana son sanin mai ya faru bayan da ya barta. Ina su innarta? Ina babanta? Me yasa ta canja daga mai tsananin wasa zuwa ma fadaciya? Me yasa ta canja daga mai son mutane zuwa me kin mutane? Mai yasa ta canja daga mai son tai mako zuwa mai kin tai mako? wata zuciyar tace ita kadaice zata baka wanan amsar. Tunanin ya katse lokacin lokacin da yaji hannun ummi a bayan shi, yasani ita ce dan suna mayukar shiri da ita. A hankali ya dago kai ya dubeta, ta tsura wa fiskarshi ido, tana da kishin yaransu kamar yanda aka san fulanin adamawa da yola nayi, da wuya kaji sunayin wani yare in ba nasu ba. Shi kuma abubakar ya fi mai da musu da turanci, haka ma abban su. Tace hamma me ya faru ne?Baka ci tuwonba kuma gashi kana ta tunani. Yayi dan murmushi tare da cewa ummi, me kika gani ne? Tace baka ci towon ba kuma gashi kana ta tunani. Yayi murmushi tare da cewa ummi kenan! Gajiya nayi yau, shiyasa kika ganni haka ya janyo tire ga banshi tare da cewa, zauna muci. Tace nikam na koshi, kaci sai in fitar da kayan, kuma bakin dada suntafi ta fito. Yace to. Ya dan tsa tsakala ya ture, ummi tace hmma ni sai nake kallon kamar ba gajiya bace, in mutun ya gaji in yayi wanka yana cin abin ci sosai, kafin yayi bacci gajiyar ta tafi. Ya dubeta ko? Tace, eh, yayi murmushi. To me ke damuna? Tace, ina kallon kamar tunani kakeyi ko? Yayi murmushi har dan sauti yafita, san nan yace to tunanin me? Ta juya hannunta tare da cewa oho. Ya lumshe ido. Ummi tana burgeshi yarinyar tana saurin fahimta shi yasa suke shiri yarinyar tana sonshi fiye da sauran yan uwanta shi ma yana yana son yarinyar, ta katse shi gashi kana sake yin wani tunanin? Yace tunaninki nake ummi, tace tunanina? To me nayi? Yace saurin fahimtar ki, tayi murmushi, to na gane cewa kana tunani kenan? Yace eh tace to tunanin me kakeyi? Ya mike zan fada maki amma yanzu muje wajen dada. Mahaifiyar tasu tana kokarin kashe TV din da rukayya ke kallo tare da yin fada cikin harshen fillanci. Na fada maki bana son yawan kallon nan, in kin gama rubutun to kije kicin kiyi min wanke- wanke. Zatayi magana sai ta fasa, saboda ganin hamma. Ta mike ta nufi kicin din. Da girmamawa ya gaida dadar su, ummi tace su ya findo sun tafi? Yace dama sune kuka ce min baki? Da na shiga mun gaisa ai, tace sune kuma saboda kaine suka zo. Anjuma zamu zauna da kai in babanku ya dawo. Ya dan ware ido, gurina? Ta nufi daki tana cewa in mun zauna zakaji, nima na gaji. Ummi ta dube shi, hamma ka zabi mata? Yace in na zaba kece zaki fara sani, ta ce zaku fara fada da dada kamar yanda kukeyi da abba. Nasani dada zatayi maka zancen aure ne, don lamido ya tarasu da baka nan kaje kano bikin abokin ka ya mai da hankali sosai gurin ta, suwa ya tara? Tace su faffa dukansu, harda fafa na abuja da abba da su gogo dukansu. Ya danyi di, tabbas ya kure kakan nasu, yau kwana 3 da dawowar shi amma ba wanda yace mashi komai? Yayi a jiyar xuciya me suka ce? Tace abba ya fada dada amma bata fada mana komai va, amma dai lalai saboda kai lamido ya hada taron, yace shi yasa tun da na dawo abba da dada suke daure min fuska har nayi zaton da na dade a kano ne musalin 9 wayar shi tayi kuka, yadaga ya duba afili yace abba. Tare da kalon hashim. Nawa zan tafi, abba na kira na. Ya dauki wayar cikin fillanci abba ke fada mashi yana jiransa, yace to gani nan. Yace nikam na boni hashim gara ka bonin, in kuma baka da lfy ne ka fada mana. Abubakar yayi dariya, kaima ka daina goyon baya na? Yace eh, na daina tunda har da iskanci, ace kaf dangi baka ga matar aure ba? Kowacce kace baka so mugashi har munyi yara. Abubakar yace, in nayi aure yan bibiyu zan haifa kaga sai in kamo ku. Ya daga murya yana cewa, shatu na tafi. Yace to ka gaida gida. Abubakar lamido shi ne da na farko a gurin ma haifiyar shi, hajiya fatima wada suke kira da (dada) da alhaji ibirahim lamido wanda suke kira abba. Duk wanda yake garin yola yasan lamido abubakar (family) saboda dukiyarsu da kuma akidarsu ta kin auran bare. Suna da yawa matuka, sam basa son su bada yayan su waje kokuma dan su ya auro, basu taba ba tun kaka da kakanni, haka suke har yau. Lamido yana da yaya kusan 30 da yankai, maza da mata. Matan sa 4 ne, kuma dukansu dangin shi ne alhaji ibrahim shi ne da na 3 gurin mahaifiyar su gogwal, wace itace matar farko, haka shine wanda ya fara yin kudi fiye da mahaifin su kafin kanansa su biyo baya. Lamido abubakar sarkine a wancan lokacin, mai fada aji, kafin ya sauka ya ba baban danshi sa‘a du maifin hashim. Lamido yanada tsutsuran ra‘ayi a kan auren waje, duk yayanshi maza saidai yace shirya kaje wajen wance yar baffanka ko yar gogonka, inko macece sai dai yace wane zai zo ki shirya ko jikokinsa haka ne abbukar su 7 ne gurin mahaifinsu,usman ke bin sa, sai umar, sai aiyu sai kasim, sanna rukayya sai auta hauwa'u, sunan gogwal ta ci suna ce mata ummi. shi ko abbukar sunan mahaifin lamido yaci, kakan babanshi kenan, shi yasa lamido ke san shi duk cikin jikokinsa yafi son baban shi abbukar kaf family hammam suke kiran abbukar don girmamawa. yana da wani irin kwarjini mai ban mamaki ga farin jini kowa na son shi, bugu da kari ya taso hannun shi sake, ma'ana yana da yawan kyauta. ya sanka bai sanka ba in yana da shi xa ya baka, shi yasa kawunan shi da goggonin sa su yafendon sa har su baffan shi kowa na son hama ya auri yarsa. su kan su yanmatan cikin family suna son sa, wasu har sun yi masa maganar, wasu sun aiko amma baice ma kowa kala ba. abbukar mutum ne da yake tsayiwa kan ra'ayinsa, a tsarinsa baya sha'awar macen da xata ce tana son shi, yafi son yaga mace da kansa yace yana sonta, matsalar shi duk cikar family bai ga wadda ta mishi ba, duk kuwa da kyawun yanmatan yana cikin maxan da kyau baya tsarin shi. a yanxu haka yana da (mastets digree) a fannin kasuwanci, yana jan kamfanonin abban su ne yayin da abban ke hutawa, tun kusan shekaru 7 bay, lamido ke zaba mishi yanmata yana cewa sai yayi master xaya yi aure. a tarihin gidan su shi ne da na farko wanda ya karya dokar lamido, ya ki yi aure a lokacin da ya bukata, bayan ya kammala karatu ya soma aiki.lamido ya kira shi yace mishi abbana, ina son ka shiga da kanka gidan baffanninka da ggonninka ka duba mata, in ma da xan zaba maka da kaina sai in ce kaje gidan baffanka na abj yaransa suna da kyau. Abubakar ya dubi kakansa, lamido nifa ba mai kyau nake so ba, kaikam sakarai ne saikace ba dan boko ba?Kowa yana son mace mai kyau, yace ban da ni, akwai wasu halaye danake son matata ta kasance dasu, a dan bani dama in tantance. Lamido yace to ubana, na baka wata 2 lokaci ishashe ya isheka kayi duk bin cikenka, abubakar yace na gode. Wata 2 har da saty 2 lanido yaji abubakar shuru, dan haka sai yasake aikowa ayi mashi kinran abubakar, wanda ya kasance cikin wanan kiran a kowanne lokacin. Abin da ya kudirta shine ba za ta taba kai kanshi gurin lamido ba, har sai lokacin da ya kirashi. Ba yan salan isha‘i ne ya sami lamido a gidan shi, cikin falonshi mai tsari irin na masu kudin da, duk da haryanzu a kwai kudin bai damu da canja tsarin falon ba, don ya masa. Ya zauna tare da gaida lamido, sannan ya sunkuyar da kai, lamido yace cikin yar tsokana, abba na nasan kana da kara ko da ka zaba mace ba zaka iya zuwa gabana ka fada ba. To dan matso ka fada mun gidan wa kaga matarka? Wacece tayi sa‘ar samun namijin duniya kamarka? Abubakar ya lumshe ido sanan ya sunkuyar da kai yace, gaskiya lamido saboda aiyuka bansamu zuwa ko ina ba. Fuskar lamido ya canja daga fara‘a zuwa daurewa. Sannan yace duk tsawon lokacin nan bakaje ka aiwatar da abinda muka zanta da kai ba, don baka dauki abun da muhim manci ba? Yace, a a yanayin aiki ne. Lamido yace yayi kyau yau wace rana? Abubakar yace alhamis, yace to gobe in an taso sallar juma‘a ka kira hashimu kuzo ina nemanku.

No comments

Powered by Blogger.