Header Ads

*** MIJIN KADDARA part5 *** ***** KARSHE ***** .

Anan zayyanewa zainab lbrn zainab tace allah sarki ga irin tanan kwadayinki dana baki shawara ai har zagi nama kinyi..zeenat tace kiyi hkr abinda ya wuce ya wuce kinyi aure..zainab tace malam hafeez na aura malamin islamiyyarmu. .zeenat tai dariya tace ahhh!! . shegiya kice saida mlm hafeez ya sameki tun muna islamiyya dama naga alama kuma naga kamar kina da abun..zainab tai dry tace ha me za'a fasa meye ajikinki..sukai ta hira har dare....bayan sati zeenat ta haihu danta namiji ranar suna yaro yaci sunan mlm adamu suke kiransa da abba..kwanci tashi yaro ya isa wata biyar ya kara wayu sosai..da rana iya abu na kasuwa gun saida abinci zeenat na zaune da yake abba ya fara zama tana zaune agabansa tanamai wasa taji yaro yayi sallama da ita wai tazo cikin zuciyarta mamaki ya kama tunda auranta ya mutu babu mai ma kallanta balle ace namijine ta ajjewa abba baby yana wasa da ita tasa hijjab ta fita kofar gida...wata mota sabuwa dal ta gani murfin motar ya bude mansur ne ya fito ya zama kato ya ajje saje afuska yayi kyau da hula fara tufafinsa ma farine sal yasha aikin sama kana ganinsa zam alhaji..gaban zeenat ya fadi zare ido tana tunanin ko amafarkine amma taga azahirine sai taji kafafunta sun kasa tsayuwa ta durkushe tamkar rakuma sai kuka..mansur ya karasu kanta ya tsaya yace zeenat meye abin kuka ki kalleni mana. . cikin kuka kanta akas taki yadda ta kalleshi tace mansur da wane ido zan kalleka idanun da suka ci amanarka suka manta dakai..mansur yace baki ci amanata ba komai ya wuce agurina..zeenat tace kaya feemin tabbas nida iyayena mun cuceka mun zalinci gashi sakayyar allah bata bammu ba sadik ya gujeni na zama mara gata acikin al umma tabbas in baka yafee mana ba wlh bamusan yaya zamuyi nan gaba ba..mansur yace na yafee muku duniya da lahira tashi ki kalleni mu shiga kinga yara sun fara taruwa suna kallanmu..zeenat ta kalleshi fuskarta ta rine da hwy idanta yayi ja dan kuka sukaiwa juna murmushi mai sanyaya zuciya....suna shiga ciki mansur yaga yaro azaune ya daukeshi yace dan waye? zeenat tace dana ne mai sunan babana abba..mansur yace allah sarki allah yaji kansa..ta shinfida musu tabarma suka zauna ta zayyane masa lbrnt agidan sadik tas shima ya sanar mata irin wuyar da yasha harya sami hankali ya shiga kasuwa anan yayi kudi sosai kuma har yanzu bashi da aure ya gama gidansa. kowa yaji rayuwar kowa sannan sukai shiru na dan mintina sannan mansur yace inaso inyi aure domin siyasa nakeso in shiga kuma kece matar...razana zeenat tayi tace haba bazai yiwu ba mansur ni bazawara ce gara yadda kake baka taba aure ba ka auri budurwa yanzu duk abinda nama arayuwa baka dena so naba..mansur yace dakata ki cewa haka kuma in kin yadda kada ki musamini ke zan aura inkin yadda domin har yanzu kaunar da nake miki na nan bata canza ba..cikin hwy tace to shikenan ka bari in yaye abba sai iya abu ta daukeshi sai ai auran ko..mansur yace a'a sati mai zuwa za'ai auranmu donna gama ko mai har kayan daki kuma ni mabukacin "ya"yana koda sunkai dubu don haka na dauki abba amatsayin dana kuma bana so ki sanar masa banine ubansa ba har sai ya mallaki hankalinsa.. . alkc iya abu ta dawo daga sai da abinci tana ganin mansur ta durkushe ta rushe da kuka dukkanmu ma harshi sai kukan dadi domin munsan rayuwarmu zatai inganci..sati mai zuwa aka daura aurena da mansur aranar na tare agidansa farin cikina ya dawo komai nama mantashi ya faru ya rikeni amana..zainab ta haifi yarta mace sajida..... . BAYAN SHEKARA ASHIRIN.................ayanzu ni zeenat shekarata 40 abba kowa shekarunsa 22 ya zama saurayi sosai fari dogo ya gama karatunsa na deegre ya suma aikin jarida daily trust harya dankara gidansa ya fara neman auren yar kawata zainab wato SAJIDA yarana hudu da alhaji mansur zuhuriyya, itace budurwa diploma take sai abdallah, sai uzaifa sai auta ta humairat......... . na samu abba na zayyana masa tarihin mahaifinsa domin besan ba mansur bane ubansa ba yayi kuka kamar ranta zai fita yace momy kina da photon abbana..nace eh na dauko masa na bashi yana kuka...... . bayan wata uku..abba na tafe amota zashi ofis sai ya hango wani tsoho tukuf da sanda kanshi gashi duk ya rufeshi har baya kayan jikinsa duk sun yage sunyi dauda abba ya kalleshi sai yaga tsohon sunyi kama da babansa da momy ta nuna masa hoton har yayi nisa sai ya juyo dakan motar.. . ya iso gun almajirin ya fito ya dauko photonnan ya duba yaga babansa ne sai kuka ya kama kuka yace baba kaine haka..tsohon yace yaro waye..abba yace adamu ne danka da momyna ka saketa da cikina..tsohon ya rungume abba sai kuka yace allah sarki dana ina zeenatun kaini gunta..ya sashi amota sai gida afalo ya ajjeta ya zaunar dashi akasa tsohon ya kama kalle kalle kamar dan kauye adam yace bari in kirata..jim kadan ya dawo yace tana zuwa..tsohon yace to yaro..sai ga zeenat da hijjab da carbi ta shigo zumbur jikin tsohon na kyarma ya mike yace zeenatu kece haka..zeenat taci dako tace sadik!! tabbas yau kaga karshenka kana tunani kudi zai kareka daga isharar allah banyi farin ganinka ba abba wayace ka kawuminshi fitarmin dashi daga falo..tsohon na kuka yace kiya feemin dana kaima kaya feemin na cuceka da tuni ka mutu ashe da sauranka kai kadai na mallaka kuji kaina. . Abba yace na yafeema momy don allah kiya feemai ko yaji sauki yauni baba daka wulakantani tun ina ciki gashi nama rana duniya kenan..hwy ya zubowa zeenat ta goge tace na yafamai halin dakema ya isheshi..ta juya tai ciki abba ya maida babansa wajen ya zaro kudi masu yawa ya bashi yayi gaba..bayan wata guda akai auran sajida da abba..zuhuriyya ansa mata rana kanwar abba ce da wani dan senator..alhaji mansur kowa ya zama babba asiyasa kowa ya sanshi ya kara ci gaba...rayuwa mai dadi ta sake kafuwa acikin da kaunar juna TAMMAT!!

No comments

Powered by Blogger.