Header Ads

***MIJIN*KADDARA part2 ***

TACE dakata me zakici da mansur meyake dashi yarinya ki kwantar dakai muci arziki mubarsa amazaunninsa..SADIK kowa yaci gaba da mana hidindimu iri iri ya dauki nauyin gidanmu ya zamana sai abinda muke so zamuci mai dadi duk shine..ni kowa na manta da wani mansur na sallamawa sadik na bashi duk kaunar dana ba mansur domin nima yana bani mamaki sanshi ya shigeni sosai..shi kowa mansur jiki yayi tsanani har tabin hankali ya samesa saboda yawan ambatar zeenat aka daukeshi sai asibitin sakatiri dake kaduna. . sadik ya daukeni da daddare muka je wani shop acikin gari ya cikomin jaka da siyayya ina sauka amota na fada gida na rungume iya abu ina dry iya abu tace wace duniyar kuka je tsiyayamin lbr..zeenat tace iya abu naso kinga shop din da mukaje saikin bata aciki turawane zallah kamar india sadik kowa yamin siyayya iya kayan make_up kawai na dubu hamsin kuma albishirinki fari ko blue..iya abu tace farin dai..zeenat tai murmushi tace muna tafe ahanya sadik yacemin ya mana visa dukkanmu har malam wannan hajjin damu za aje..iya abu tai ihu ta kankame zeenat tace mun gode sosai kice saura wata uku mu hajiyance..ranar kwana sukai sambatu dam murna..malam ya kira sadik yamai godiya sannan yace yaso ai maganar aure da wuri dan danan akasa rana wata biyu aka kawu lefe akwati takwas kaya sun hadu an zuba karya domin kayan cikima odarsu akai daga london.. . zeenat na bakin mirror tana tsantsara kwalliya zainab ta shigo ta zauna zeenat tace kawata lfy..zainab tace zeenat yanzu don allah da gaske kin amince da sadik amatsayin masoyi..zeenat tace kwarai kowa wayaki dadi duba bayanki zakiga lefenmu kuma saura sati mu tafi makkah hajji harsu mlm..zainab ta kalli akwatinan aharare tace kin kyauta amma koki sanarmin saboda kinsan baki da gky yanzu ashe dama soyayyar da kikewa mansur ta karyace har kudi zaisa ki mance da halaccin daya miki arayuwa shekararku uku wlh shine msyk nagari amma kin cika butulu..zeenat tace kada ki gayamin magana me zanyi da mansur ni masara shi dawa idan anyi auran muci babu ga maishi ahannu kuma na tabbata sadik miji ne mai tausayi miji na gari..zainab tace allah sarki talaka mansur na tausayama duniya ta gaji haka inaso ki sani bani bake har abada mayaudariya kiyi ki gani shashasha..ta suri jakarta ta fice zeenat ta harareta tace akuya dabba kawai kai duniya ba daba aga cigabanka sai kaga hassada afili allah ya rabani dake lfy... . sati na zagayuwa muka tafi saudia mukai hajji watanmu guda muka dawo mun canza munyi fresh mun goge dan danan malam ya tsaida ranar bikinmu sati na uku na zuwa aka daura aurena da sadik sulaiman ni kuma zeenat m adam akan sadaki dubu dari anyi wadaka naira tai kuka dare nayi mukaje tropical hotel dinner party washe gari aka kai amarya akano g.r.a anguwar attajirai cikin wani katan gida tamkar aljannar duniya..sadik yaci gaba da nunamin kauna iri iri duk inda nai yana bina kamar gam..ina kitchen ina girki sadik ya shigo yace oh ashe kina kitchen duk na duba bangankiba..zeenat tace gani meza kamin..sadik yace tayaki girki zanyi kinsan inban gankiba bana iya jin dadi. . zeenat tai dariya tace ok ngd to inna mutu fa?..sadik yace sai na biki nima..bayan biyu..zeenat na zaune tana tunanin halayen sadik domin ya kasance akowane dare kansu kwanta saiya bata wasu kwayoyi na magani yace tasha inta karba saita fito falo ta zubasu acikin wani kwano mai murfi yanzu kwanon ya cika dam da kwayoyi ita kuma bata taba tambayarshi dalili shi kuma bai taba sanarmata ba tana tunanin wannan wanemagani ne?me yake so ya mata dayake duramata duk da batasha meye ma'anar hakan amma ta kasa ganu mafita..sadik ya shigo yace amarsu tun dazu ina jiranki aroom ga maganin kisha ki sameni abed..ta amsa sai da yawuce ta dubeshi cike da tunani ta bude kwanon ta watsata dauko swan tasha kawai ta bishi.....bayan sati..zeenat na kwance agado zazzabi rum sadik ya dawo daga ofis yazo kusa da ita ya taba wuyanta yace my hearth what happenmeyasa kike wasa da lafiyarki dakin sanarmin..zeenat tace kada hankalinka ya tashi shi yasa wlh dazuma amai nai tayi..sadik yace oh sorry tashi mu tafi asibiti..sai da nai wanka na tsala kwalliya kamar bamai cuta ba illah jikina da nakeji ba kwari nahau gaban mota sai wani asibitin abokin sadik muka isa osmosis hospital akamin text muna zaune akujeru kalid yazo da resulta yace sadik ina tayaka murna da jin dadi matarka na dauke da ciki na wata guda..mmurmushi nai ina murna amma zumbur sadik ya mike idonshi azare yace ciki!!! kalid yace yes ko baka murna ne..sadik ya kalleni yamin wata harara sai naji gabana ya fadi sosai ya fice afusace cikin sauri.....

No comments

Powered by Blogger.