Header Ads

SANADIN BOKO 3-1

Abubakar yace to. Lamido yace tashi kaje, bai amsa sai anjuman da abubakar yace masa ba. Duk da abubakar na sane yaku ma dawo gida daga ofis, bayan salar juma‘a sai ya kishin gida har dan bacci ya soma daukar shi, sannan yaki kiran hashim ya fada mashi kamar daga sama sai yaji an doki kafadar sa, ya bude ido yaga hashim tsaye, yace har ka iso? Hashim yace na iso ina? Ka fada min ne? Yanzu lamido ya kira wayata yace ya yajimu shuru. Nace me yafaru? Yace baka famun yana neman mu ba. Na kareka nace ka fada min, nace na mantal yace ya bamu minti 20. Abubakar yace kanme zakayi karya? Kawai kace masa ban fada maka ba. Hashim yace tashi dai muje, amma bari ka canja kaya, ya bude duriwar manyan kaya ya ciro masa shadda waganbari bowa mai kalan sararin samaniya. Hula baka minister, ta kalmi baki, yace tashi dan Allah fadan lamido bashi da kyau, tunda in ya tashi sai ya fara cin uban iyayen mu kafin ya dawo kan mu. Abubakar ya soma sa kaya yana cewa, ni nifa kasan Allah? Eh inji hashim, babu mai min auren dole. Sai irin matar da tai min, mace 1 nakeso a rayuwata, kuma sai na zabi duk wadda ta hada duk irin halayen da nake son don bana son inyi mata 2 ko 3, 1 nan ta isheni. Hashim yayi dariya, sanan yace niko har na hango wace zan kara da ita fatana Allah karyasa lamido yace wajenta zamuje. Abubakar ya dube shi kana nufin wai lamido zai ce min in je gurin wata ne? Hashin yace kaima ka sani, domin in baka manta ba juma‘a kamar haka yace kasameni muje gunsa, mukaje yace muwuce wirin shatu. Kana nufin munfika biyaya ne? Kada ka manta mahaifiyar ka da a haifin ka yar mace da dan namiji suke, kuma suma hadin ne. Abubakar yace duk ina sane, hasim kanayi kamar baka san ABUBAAR SADDIK ba, zaku sha mamakin zuri‘ata tashi muje Hashim ya mike tare da ajiye kwalbar turaren da ya kara fesawa a mazauninta. Duk suna zaune gaban Lamido, wanda fuskarsa ke take, yace Hashimu kuje gidan Baffanku Adamu, 'yan matan gidan guda biyu ne, ka zabi daya da kanka ina jiranku bayan sallar isha'I". Hashim yace to, mun gode. Sai mun dawo. Suna mota Hashim na tuki, Abubakar yana ta son tuna 'yan matan gidan Baffa Adamu. Anya ya san su ma? Hashim ya katse masa tunani da cewa, "Kai duk ruwan idonka saika zabi daya daga cikin yaran gidan Baffa Adamu." Abubakar yace ba dole bane su min. Hashim yace Allah yasa kada ka canki wadda nake hari." Tsaki Abubakar yaja, sannan yace tun kana yaro zaka tara ma kanka gajiya, ka hada mata suyi ta maka rigima kullum kuna fada Lamido, gashi kai ba dama ka saki wata duk danginka irin gidan Yaya Sule gida sai kace sansanin yaki." Hashim yayi dariya harda dukan sitiyari, sannan ya ce ni nan sai na gaji Lamido hudu nan sai na hada, Allah ya taimaka inji Abubakar. A kofar falon suka yi sallama, Yadikko ta amsa tare da bude kofar, ganin su Abubakar ta fadada fara'arta, tana masu sannu da zuwa cikin harshen fillanci. Sun zauna a falon suka gaisheta, ta amsa tare da tambayar mutanen gida, suka ce lafiya, cikin hanzari ta nufi dakin 'yan matanta guda biyu, tace Maimuna ga baki can falo su Hamma ne ku kai masu abin sha. Jamila ta mike da hanzari, haka ita ma Maimuna kowacce tana fatan gurinta yazo. Tun fitowar su ya tsaida hankalinsa gurinsu, tabbas da don kyau zaiyi aure da ya zaba, amma ba ra'ayinsa kenan ba. Cikin yanga Maimuna ta gaishe su, yayin da Jimila keta rawar kai gami da tsuga surutu. Maimuna kam tun daga gaisuwa ta ciro waya tana ta yin abinda bai sani ba, chattin ne ko game. Hashim yayi kasa da muya yace wacce tayi? Kafin Abubakar ya bada amsa, Jamila tace Hamma don Allah inga wayar ka. Ba tare da ya bata wayar ba ya mike. Hashim tashi lokacin sallah yayi, ya dube su ku kira ta muyi sallama. Maimuna ta dube su har zaku tafi? Ko ruwan kai Hamma baka sha ba. Yace zan sha wata rana, yau kam na gode. Yadikko suka jero da Jamila nan dai suka yi masu sallama, a hanya ne Hashim yake ta damun shi da son jin wacce ya zaba, yace ni fa babu wadda tayi min. Hashim yace don me? Ga Jamila, Abubakar yace bana som mace mai yawan surutu da rawar kai, gami da bincike, wannan ya nuna in na aureta zata dinga daukar wayata tana min bincike ko kuma tana min bincike a daki. Ya ce, Maimuna fa? Ita ma a'a ban cika son mace mai shiru sosai ba, sai yawan danna waya, hankalina bazai kwanta ba, domin zata iya share ni tayi ta mu'amularta da waya. Hashim yace, tab, to wallahi bada ni za a gurin Lamido an jima ban don haka kaje ka masa bayani. Abubakar yace tare zamu je, zaka ga kamar bazan iya yi masa magana ba ko? Hum, bari mujem suna gaban Lamido duk sun yi shiru, shi kanshi Abubakar yana jin zuciyar shi na rawa, tamkar bazai iya bayani ba. Amma ya daure yace babu wadda ya zaba, ya kawo dalilansa. Lamido ya tsura masa ido, zuciyarsa na zargin Abubakar nason kawo masa sabon salo ne cikin zuri'a, amma sai ya danne yace naji. Hashim tun daga gobe Asabar har zuwa rana irin ta yau, ku zaga duk zuri'ar mu Abbab ya zabi wacce yake so in na Yola basuyi ba ku tafi har Adamawa, kai har 'yan Kaduna da Abuja da Kano kuje ya zaba. Tsahon sati biyu na baku, ina jiran amsa. Abubakar yace to mu gode sai dai a duba yanayi ayyukan mu. Lamido yace wannan ya rage naku, ku zaku cire lokacin da kuka ga zai dace ba tare da kun shiga lokacin aikin ku ba, ku tashi kuje. Sun ajiye bayan isha zasu dinga bin dangin kila a dace. Sati guda suna zagaye gidajen dangi, amma ko ina sai Abubakar yace bata yi ba, wannan yace kazama, wannan yace zatayi rowa, wannan yace ta cika yawo. Hashim yace to muje gidan mu ga kanne na, su kuma yace basa jin magana, irin su daya da Rukayya kanwata. Hashim yace haka ne amma fa bazaka samu mace dari bisa dari da irin halin da kake so ba, su dama da kashin hakarkari akayi su kaga kenan a karkace suke, in ka dage cewa zaka mikar dasu sai su karye. Abibakar yace, look bance maka dama ba, amma irin matar da nake so nasan zan samu. Hashim yace kasan me zamu yi? Tunda yau goma ga watan daya, saura kwana biyar ayi family meeting mu jira ranar in kowa yazo sai ka duba Abubakar yace Allah ya kaimu Duk shekara suke yin mitin na zuri'ar su, suna yin taron ne a gidan tsohon wato Lamido, suna tattauna matsalolin 'ya'yansu da su kansu a taron, duk wata kowanne mai matsala yana fada ta kudi ko ta wani abin da yake suna da asusun da suke tara kudi duk wata. Sai a dauka ayi maganin matsalar da shi, tunda kuma ba duk dangin bane masu kudi, sai dai masu kudin sunfi talakawan yawa. Tun ana gobe taron ake kada shanaye biyu saboda yawansu, Lamido ke bada su, yayin da wasu daga cikin manyan 'ya'yan zasu yi ta kawo kulolin abinci manya kala daban daban, yan nesa irin su Abuja Kaduna tun Juma'a suke dauko hanya. Dada ta shiga dakin bayan ya amsa sallamarta, ta ta ganshi kwance cikin bargo kasancewar lokacin sanyi ne tace, ka tashi fa Abban ku fa ya tafi dasu Ummi da Aliyu da Kasim. Usman da Umar kuwa na tabbata yanzun sun tafi da iyalansu. Shiri yayi tsaf cikin kayan alfarma, in ka ganshi zaka yi zato cewa sarki ne, shi da Dada ne kadai. Gidan ya cika makil, filin da aka saba yin taron tuni an shirya shi da kujeru, gurin zaman iyaye daban, na 'ya'ya daban haka ma na jikoki. Dole su baka sha'awa, yanmata da samari ga sunan, wasu dama anan suke hada kansu shikenan, Lamido hakan na daga cikin abinda yake sashi jin dadi a taron, gurin su Hashin Abubakar ya nufa, a gabaki dayan tsararrakin sa babu wanda bashi da yara........ har saitin su usman da umar duk sunyi aure, hatta usuma da umar suna da matansu matar usman tana da tsohon ciki, ta usuman kuwa tana da danyen goyo, dukansu suna aiki ne a kar kashin abubakar don mutun ne mai adalci, kansu umma a hade yake. Hashim ya soma yi mashi tsiyar cewa ya makaranta, salisu yace ba dole yayi maka ba, tun da bashi da mai tashin sa. Sani yayi tsagal yace, azumin nan mai zuwa sai munyi mashi kidan tazuru, yace zakuyi ku gama. Hashm ya turo mashi kujera zauna dai dai nan ka samu damar kalon yan mata gasunan iyaka gininka. Ya zauna tare da cewa ku tayani duba, sun bude taro da adu‘a kamar yanda suka saba, sannan aka gabatar da marasa lafiya dan ayi masu adu‘a sannan sauran abubuwan suka ci gaba. Daf da karshene wanin baffan su mai suna yusuf yace ya kamata kafin a tashi daga taron nan a saka ranar abubakar, dan kowa ya san lokacin, duk iyayen sun amince da hakan. Lamido ma yayi na‘am. Abubakar dai zuface ta rufeshi, yayin da a bokan wasa suka ta masa dariya. Sukuwa yan mata kowace tana son taga wacece mai rabon nan. Shi kuwa tuni taron ya gundire shi. Anci ansha samari sun sami yan mata wasu kuma sunyi kari, amma abubakar duk basuyi masa ba. Hashim yace gasu khalisat yayan baffa na abuja, yace wadan nan yaran masu salon tsiya, barni kawai. Kamar daga sama yaji lamido na kiran shi tacikin abin magana, Hashim yace to kaifa kila yau ta yan tatsuniya za a yi maka, irin na 'ya'yan sarakunan nan ace mata su jeru namiji yaje ya zabo. Abubakar ya mike ya mufi gurin Lamido, yace ina so yanzun nan ka shiga cikin 'yan matan nan yanzu ka fitar da mata ka, nasa ranar auren ka wata biyar daya ga watan. In kayi lissafi zai zama wata hudu da kwana goma sha biyar kenan, kafin lokacin kun fahimci juna." Nan da nan dangi suka sheda suka shiga murna, shi kuwa gurin zaman shi ya koma. Hashim yace tashi mu duba, yace dan Allah ka bar ni ka ji." Haka taron ya tashi ba tare da Abubakar ya zabi mata ba, hakan ya kona ran mahaifansa da Lamido, daga bisani kakarsa Gogwal kodai bashi da lafiya ne? A bincike shi, sun tsare shi ya ce shi kam lafiyar shi lau, amma bai samu kawai mai irin halayen da yake so bane. Cikin bacin rai Lamido ya ce sun zura masa ido amma ya sani rana baza a daga ba ko ya sami mata ko bai samu ba, in lokacin yayi zasu daura aure da duk wadda suka ga dama. Abubakar kuwa ko a jikinsa, cikin hakan ne bikin abokinsa Sagir ya taso a Kano, yaje yayi arba da yarinyar da ya santa a Kaduna lokacin da yaje (Bautar Kasa), tana talla mai yawan wasa, kusa shekaru goma baya. Yana son sanin abubuwa game da yarinyar kuma yana jin wani abu a ranshi game da ita, sai dai abin tambaya ta tara halayen da yake so matar shi ta kasance? Ya iso gida daga gida Hashim, gaban iyayan nashi ya zauna a kasa, Abban ya dube shi yau in ni na haife ka ina son ka fada min nufin ka damu. Dada tace dazun su Yafendon shi da suka zo dukan su kowa na cewa yazo ya sasanta da 'yar gidanta, na ce masu dai kun sanshi in ya yarda shike nan, amma fa ni bazan maku alkwarin ko ya yarda ba. Don haka ka fitar da mata kada ka hada ni da 'yan uwana, Abba yace yama fada mana nufin shi kawai, in yana da wata matsala ne sai ya kawo uzurin sa muji, in ko lafiyar shi lau to raini ne da walakanci, baka jin kunya kannan ka duk sunyi aure cikin dangi ko ina lbarinka ake, fada min nufinka." Ya danyi dim don yasan abinda zai fada yanzu zaya girgiza su. Dada kayi magana mana. Ya dan numfasa yace, naga wadda nake so." Abba yace, ko kai fa, fada min wacece yanzu na sanar da Lamido ta waya." Yace tana Kano." Suka hada baki gurin cewa, Kano? 'Yar gidan Goggonka Furera?" Ya ce a'a ba dangin mu bace. Suna hada baki gurin cewa, ba dangi ba? Eh, ya dago ya dube su, ba zato sai yaji saukar mari gefe da gefe, sannan ta rufe shi da duka. Sunkuyar da kai kawai yayi tayi ta dukan shi. Abban su kuwa sunkuyar da kai yayi ba tare da yace Dada ta daina dukansa ba, har sai da ta bar shi don kanta. Cikin tashin hankali take cewa ba zaka jawo mim abin fada a cikin dangi ba, kai ne mutum na farko da zai kawo matsala a zuri'ar mu? Tur! Ba dani za a yi ba, ta fice daga falon rai bace, yana nan zaune Abba yace kasan dai kazo da abin da bazai yuwu ba ko? to ka cire wannan tunanin a ranka in dai kana so kaci gaba da zama danmu. ya mike shima ya fita dàga falon, Abubakar yana zaune cikin halin da baza yace gashi ba, yafi awa daya saññañ ya fito ya tafi dakinsa. washe gari sam iyayen basu amsa gaisuwar sa ba, wannan lamari ne mai girma. Ya zama dole ya faranta ran iyayan sa, yasan idan tasu ne zai iya shawo kan su, tsoron lamido da sauran dangi suke yi. Shi kuma yana so ya kawo karshen wanan auran, domin wasu na cutuwa, an hada su da wadanda basu so. Sannan ko mai mace zatayi wa namiji ko shi yayi mata babu rabuwa, yasan ba wai haramun bane auran zumuncin, to amma yanda zuri‘arsu suka dauke shi tamkar ibada, shine yake son su gane auren bare ma ba haramun bane. Akan gadon shi yake ta juyi tare da neman mafita, ya kalli agogo 11 a fili ya furta Allah yasa hashim bai yi bacci ba, ya daga wayar sa yasa a kunne, bayan ya laluba num hashim din. Tayi kuka har ta katse ba‘a dauka ba, don haka ya ajiye wayar yana miyar hashim har yayi bacci sai kace mace. Kusan minti 30 wayarshi ta soma ruri, ganin sunan hashim ya daga da wuri,ya soma korafi ka cika baci kamar mace. Hashim yace ina tare da iyalina ban san tayi ringin ba, duk da tana kusa dani in ka fahimce ni ka kira lokacin ina duniyar ma‘aurata, bana tare da ku. Abubkar yace ban tam bayeka ba, sannan Allah dai ya tsine ma mai tona asirin iyalansa, don haka sai kai hattara. Kasanan dalilin kiran da nayi maka? Hashim yace sai ka fada? Abubakar ya gyara kwanciya sannan yace, kila kaji mamakin cewa wadda nake so ba a cikin zuri‘armu take ba ko? me kake son fada mun? Hashim ya mike ya nufi falo dan kada matarshi shatu taji abin da zasu tau tauna. Kada kace zaka shugo da bidi‘a cikin zuru‘ar anan, kasan hakan zai jamaka matsala kai da mahaifin ka? Abubakar yace haba hashim kai fa ba jahili bane, abinda kake kira bidi‘a ba haramun bane. To auren zumunci sunna ne? Ka fada mun a matan monzon Allah wacece yar uwarsa ko a kwai bata wuce guda 1 ba, kuma duk matansa yan kabilar sa ne?Dashi fa muke koyi, don haka matar da aura ina nufin ba haushiya ce, ina zoton ma ba zawara ce, kaga kenan zanyi sunna. Hashim yayi tsaki, wannan karan bana tare da kai, matsawar baka canja tunani ba. Me hausa sukafi yaren mu na fulani? Kyau ko asali? Abubakar yace look! Hashim ka fahim ceni sosai, ba al‘ada ce a gabana ba, addini nake son awa agabana, yarenmu suna da kyau da asali da kuma tarbiyya, amma ban ga wadda tatara irin halin da nake so ba. Ok inji hashim. Ita wannan ta tara duk abin da kakeso? Abubakar ya tashi zaune, ba zan saniba sai dai na ga 1 daga ciki, saura sai ta bani dama mun zanta. Hashin yace kana nufin baku taba zantawa ba? Abubakar yace ni ke sonta, ita bata san inayi ba, domin bata so in kusanto ta, na dai taba sanin ta da. Hashim dan Allah ka natsu, ina so ka taimaka mun yanda zan shawo kanta, zanfi tsayuwa kan ra‘ayi na inna tuna wanda nakeyi dan ita, ta san ina yi. Hashim yace, abinda zai fi kaje ka fada mata nufinka, ka ce mata kana sonta kuma zaka aure ta, na san zata girmama zan cenka don matan da suka san abin da suke yi, suna girmama zancen aure. In dai ba wani ya riga ba. Abubakar yace ta tsani maza, ina zaton namiji yayi mata laifi. Hashim yace kaje, in baku sasanta ba ka sanar da ni, sai mu koma tare. Kai dai kasan yan da zakayi mahaifanka kada su shiga fushin lamido. Yace zan ga me zanyi. Sukayi sallama. Arana ta 3 ce daada ta shigo dakin shi, da wowarshi kenan daga office, tace ka sauya ra‘ayin ka ne ko kanan kan bakanka? Ya kwantar da murya. Dada kiyi hakuri, wlh wace nake son aura musulma ce mai tarbiyya. Tace amsa kawai zaka bani, ba. Tace amsa kawai zaka bani, bana son dogon turanci, ya ce to duk yanda kuke so haka zanyi, tace uhm! Isa da kai kaje ka cire mata a dangi, ta tausasa murya, da zakaji tawa ma, ka sami lamido ka fada mashi ya zabo maka. Na tabbata zaka wanke lefukan da kowa ke ganin ka dashi. Muma zaka ciremu a zargin da lamido ke mana, na san baka sami lbr mitin din da lamido ya kira su abban kuba ko? Ya dube ta, na sami labari sai dai ban san abun da aka tau tau na ba, duk da nasan dan ni akayi shi. Tace to ya tara yayan shi maza ya sanar dasu cewa bai yafe ba duk wanda ya bari dan sa ya kawo bakon lamari a cikin zuri‘armu ba, yace za‘a yanke mumunan mataki a kanshi da yayan ta hanyan yanke zumunci da su

No comments

Powered by Blogger.