Header Ads

====== 01. ====== HIKAYAR TAJIRI DA IFIRITU

1467290-229258477249958-1.jpg A zamanin da, a wani babban gari, an yi wani babban attajiri, mai yawan dukiya, mai yawan tausayi da taimakon talakawa. Wata rana attajirin nan ya fita bayan gari yawo shi kadai domin shan iska, sai ya tsaya domin ya huta a karkashin wata itaciya mai sanyin inuwa. Ya fito da gurasa da dabino da ruwa daga cikin jakarsa, domin ya ci ya kuma sha ruwan kafin ya wuce gaba. Bayan ya gama cin gurasa sai ya dauko dabino yana ci. Yana cikin cin dabinon nan sai ga wani Ifiritu (aljani), mai girman jiki, tamkar itaciyar kuka, mai tsayin gaske, tamkar itaciyar rimi, da jajayen idanu, tamkar garwashin wuta. Ya fito rike da takobi a hannunsa, ya ce da wannan attajiri, tashi in kashe ka tamkar yadda ka kashe dana. Tajiri ya ce, “Ta yaya na kashe danka?” Ifiritu ya ce, “Yayin da ka ci dabino ka yi jifa da kwallon ya sami dana a kirji har ya fadi ya mutu. Babu makawa yanzu in dau fansa, in kashe ka tamkar da ka kashe shi.” Tajiri ya ce, “Ka sani ya kai wannan Ifiritu akwai bashi mai yawa a kaina. Ka bar ni in tafi gida, tsawon shekara guda, in bai wa dukkan mai hakki hakkinsa, sannan in komo nan ka aikata abin da ka yi nufi a kaina, za ka same ni mai cika alkawari, haka Allah ya kaddara.” Ifiritu ya yarda da bukata tasa. Tajiri ya komo gida, ya fada wa iyalansa da danginsa da abokansa dukkan abinda ya faru da shi, suka yi ta kuka, kuma ya biya dukkan mai bin sa bashi hakkinsa. Bayan shekara guda ya koma inda suka hadu da Ifiritun nan ya zauna yana jiran fitowarsa. Yana nan zaune yana jiran abinda zai same shi, sai ga wani tsoho tafe, ya na jaye da barewa, da igiya a wuyanta. Ko da tsohon nan ya iso wurin tajirin nan sai ya ce masa, “Bawan Allah, me ya zaunar da kai wannan wuri? Hala ba ka san cewa wannan wuri matattarar aljanu ba ne?” Tajiri ya kwashe labarinsa da Ifiritu ya fada wa tsoho. Tsoho ya ce, hakika labarinka akwai ban al’ajibi da tausayi a cikinsa. Lalle ba zan bar nan ba sai na ga abinda zai kasance a gare ka. Ya sami wuri ya zauna. Suna nan zaune, sai ga wani tsoho tafe ya na jaye da karnuka, bakake guda biyu. Tsoho mai karnuka ya yi sallama gare su. Bayan sun gaisa, ya tambaye su labarin zamansu wannan wuri wanda ya ke matattarar aljanu. Suka fada masa abinda ya ke faruwa. Da ya ji haka sai ya ce, lalle ba zan wuce ba har sai na ga abinda zai faru tsakanin Tajirin nan da Ifiritu. Ya sami wuri ya zauna. Tsohon nan mai karnuka bai gama zaunawa ba, sai kuma ga wani tsoho tafe akan wata alfadara ramammiya. Da tsoho mai alfadara ya iso ya yi musu sallama, suka gaisa sannan ya tambaye su dalilin zamansu a wannan bigire. Suka labarta masa abinda ke faruwa. Shi ma ya ce ba zai wuce ba sai ya ga karshen wannan al’amari. Ya sami wuri ya zauna. Tajiri da tsofaffi na nan zaune sai suka rika jin wata irin hargowa, mai cike da rugugi da tsawa da iska mai tsanani tana kadawa, kasa kuwa kamar za ta tsage saboda rugugi da kugi. Kura ta tashi ta murtuke ko’ina, ta rufe hasken rana, ba a ganin komai tamkar a tsakiyar dare. Yayin da hargowar nan ta lafa, kura ta yaye wuri ya koma dai dai, sai mutanen nan suka ga Ifiritu a tsaye da takobi zararre a hannunsa, idanunsa ja wur tamkar garwashin wuta. Ya fizgo Tajirin nan daga cikinsu ya ce, tashi in kashe ka tamkar yadda ka kashe dana, sanyin zuciyata, farin cikin rayuwata. Tajiri yana kuka yana kururuwa da hargowa, tsofaffin nan su ma suka fashe da kuka domin tausayin Tajiri. Sai tsohon nan na farko, mai barewa ya matso kusa da Ifiritu, ya durkusa ya ce, “Ya kai wannan Ifiritu, Sarkin Sarakunan aljanu, da za ka tsaya in ba ka labarina da wannan barewa da nake tare da ita, da ka ji labarin abin al’ajabi wanda ba ka taba jin irinsa ba, amma sai idan ka yi alkawarin za ka ba ni wani yanki na jinin wannan Tajiri.” Ifiritu ya ce, “Na yarda idan ka ba ni wannan labari na ga ya kasance abin al’ajabi da mamaki zan ba ka sulusin jinin wannan mutum.” Tsoho mai barewa ya yi godiya ya fara ba Ifiritu da sauran mutanen da ke wurin labarinsa, da abin da ya kasance a gare shi tare da wannan barewa, kamar haka:......

No comments

Powered by Blogger.