Header Ads

ANA WATA GA WATA

Wani malamin Kirista (pastor) yace "Da ace ranar tashin Qiyama za'a bashi daman kaiwan mutane wuta da Al-jannah to zai dauki mazan musulmai masu aure ya kaisu Aljannah, matan su kuma zai kai Jahannama, aka ce me yasa kace haka? sai yace matan musulmai suna zaune a gida mazajen su suke musu komai, su kashe musu kudi suyi wahalhalu amma idan yaje gida sai tace masa ni me ka taba mun? banda wahala me nakeyi a gidan nan? paston yace "idan ba jahannama ba ina ya kamata akai irin wadannan" yace "amma kaga matan kirista to su kuma Aljannah zan kaisu, mazan kuma na jefa su a Jahannama saboda kirista zai auro mace amma ba ruwan sa da cin ta da shan ta, bai damu da ita ba, sau da yawa ita zata je gona ko wurin sana'a ta nemo abinci, idan tayi magana kuma ya mata mummunan duka kamar baiwar sa, amma sai tayi hakuri a haka, paston yace to idan ba Aljannah ba ina ya kamata akai wadannan matan? to 'yan uwa wannan magana abin dubawa ne duk da dai akwai shirme a maganar, menene ra'ayin ku akai? ---

No comments

Powered by Blogger.