Header Ads

WANI MA,AIKACIN GIDAN MAHAUKATA YAYI HIKIMA!!!

A duk karshen kowace shekara ana canza fentin gidan mahaukata haka kuma ana canza duk wasu abubuwa da suka lalace kamar kofofi ko fanfuna na diban ruwa dadai sauran su. idan za'ayi irin wannan aikin to gaba daya ranar za'a sa mahauka tane a mota a dan kewaya gari dasu saboda suma su dan sha iska,kuma kafin su dawo an gama yan ayyukan da za'a yi a cikin dakunan su a irin wannan rana ne shugaban gidan mahaukatan ya kira wanda zai dauke su a mota domin su zagaya zuwa offis dinsa shugaban ya dubi direban yace''kaga dai bala kai sabon ma,aikacine anan gidan kuma yaune zaka fara wannan aiki,saboda haka yanzu idan an saka mahaukatan nan a mota kun tafi,to duk abin da zasu ce maka kada ka bude kofar motar nan, kaji ko'' bala ya dubi ogan yace ''na fahimta-ogan ya sake cewa''kome fa asu ce maka kada ka bude fa''bala ya kara cewa''naji oga ba matsala Aka zuba mahaukata a mota bala ya tuka ya tafi dasu sai da suka shafe kusan awa biyu yana ta kewaya gari dasu a cikin mota sannan sai suka fara bubbuga jikin motar suna magana bala yaki kula su saboda ammai gargadi da suka cigaba da tafiya har sai da suka wuce dambatta sannan suka cigaba da bubbuga motar suna ihu-a dole bala ya tsaya ya sauko ya leka ta wundo yace musu''wai meye ne?'' yaji daga cikin motar dukansu sunce''fitsari muke ji''har bala zai koma ya tuka ya tafi sai yaji wani ya fashe da kuka acikin su,saboda haka sai ya tausaya musu ya sake lekawa ta wundo yace''to nayarda zan bude muku amma sai dai da daidai zaku dinga fitowa kuna yi kuna komawa'' mahaukata suka ce sun yarda Bala yana bude kofar suka fito gabadayan su daga cikin motar kowa yayi hanyar sa bala ya tsaya ya rasa wanne zai bi har suka gudu dukansu nan da nan bala duniya tamasa zafi ya rasa mai zai yi kawai sai ya tsugunna yana cizon yatsa gashi kuma lokacin komawa da aka basu ya kusa kuma duk sun gudu yanzu ya zanyi? Bala ya tambayi kansa sai da bala yakai kusan minti ashirin a zaune sannan dabara ta fado masa kawai sai ya shiga cikin motar ya tuko ta zuwa dai dai kasuwar danbatta yayi fakin dukka ga fasinjoji nan suna jira mota sai bala ya fito daga motar sannan ya bude kofar da ake zuba mutane sai kuma ya dubi mutanen da suke jiran mota agurin ya wage muryarsa yace ''INA MAI ZUWA KANO YAZO NAIRA ASHIRIN ASHIRIN-KANO MURATALA MURTALA'' Kafin kace kwabo tuni mutane sun ciki motar nan shikuma bala yana gefe yana kirgawa suna cika adadin mahaukatan nan sai ya rufe kofa ya shiga gidan direba ya tuka ya tafi dasu bai tsaya a koina ba sai agidan mahauka ta sannan yayi birki!!! Hmmm Kunji hikimar bala.

No comments

Powered by Blogger.