Header Ads

BAKIN ALKALAMI

Part 4 Da lokacin sallah yayi tashiga toilet din domin yin alwala amma ta kasa kunna koda fanfon bayin haka ta fito ta nufi falo ko Allah zaisa taga hajiya ta fada mata takasa kunnawa tsayawa tayi tanata faman kallon makekiyar plasma TV din datake manne ajikin bango tana tayi kamar ka kira mutum ya amsa dan girma anan tashagala har hajiya tafito lokacin ta canja shiga da wata sabuwar shadda wacce tasha dinkin surfani wuyanta kuma tasaka wata dankareriyar sarka ta azurfa sabanin dazu datake sanye da jar atanfa da sarkar daham fuskarta dauke da fara"a tace amna kallo akeyi ne? Eh dama hajiya alwala nake sonyi kuma nakasa kunna fanfon dariya hajiya tayi tace to zomuje kiga yadda akeyi bayanta tabi suka nufi toilet din acikin ranta kuwa cewa take ko ina wannan yar gayun ta dazu? A haka suka shiga ta koya mata yanda ake kunna komai ta fito tabarta alwala tayi tazo ta shinfida sabuwar dardumar da taga hajiya ta ajiye mata harda katon hijabin sallah,tana idarwa tafara yiwa iyayenta addu'a tareda yiwa kanta addu'ar samun zaman lfy acikin wannan gida. Hajiya dakanta taleko tace taje cikin kitchen ta dauko abincinta taje tadauko acikin wani flask mai kyau tuwon semo ne miyar danyar kubewa yasha kaji da ruwan roba mai sanyi tuni amna tafara ci tana santi. Washe gari da safe tatashi da wurwuri taje ta gyara falon ta koma kitchen ta hada kwanukan ta wankesu sannan tashare cikin kitchen din goge gogen kayan cikin kitchen din tafara tsawa taji andaka mata wacce har saida taji hanjin cikinta ya kada matsa tace da ita da sauri tajiyo budurwar nan tajiya taga tana sanye da kayan bacci doguwar riga kanta babu dankwali sai gashinta data hada tadaure wuri daya dasauri tamatsa tabata wuri fridge ta buda ta dauko lemon gwangwani tajiyo gareta tace ke bar abinda kike kibiyoni cikin rawar jiki ta cillar da tsumman dake hannunta tabita jikinta yana kyarma.

1 comment:

Powered by Blogger.