Header Ads

BAKIN ALKALAMI

Part 3 Tuni itama yarinyar tafara kwalla matar gidan ta bude jakarta dake kusa da ita tafito da rafar kudi yan dari biyar biyar ta kirgo wanda ni ummi Aisha ban san yawansu ba ta mika mata tace kigaida gida sai kinga aike tace to nagode hajiya kuma harda wahala nagode nagode tafita daga falon, tana fita hajiya ta maido da hankalinta kan yarinyar wacce taketa faman kalle kallen kayan more rayuwar dake cikin falon idan bata manta ba falo nafarko kalar kayan dake cikinsa komai sky blue ne falo na biyu kuma komai naciki red ne shikuma wannan gashi komai ash colour lalle masu kudi suna shagalinsu matarce ta katse mata tunaninta tace yan mata meye ma sunanki? Cikin ladabi da girmamawa tace Amna kai tagirgiza tareda tausayawa yarinyar dan taga bazata wuce 18 ba kinyi makaranta? Ta tambayeta eh nayi primary har secondary ma nagama bana, tace to kina jina dasafe idan kin tashi zaki gyara falo kuma zaki gyara min kitchen kinji? Ta daga kai alamun to tace zomuje na nuna miki inda zaki zauna ta mike tana gaba tana biye da ita abaya har wani dan nadaidaicin daki wanda akasaka dan karamin gado aciki sai wardrobe da mudubi da toilet aciki tace ga dakinki kinji? Durkusawa tayi tafara cewa hajiya nagode Allah yasaka da alkhairi saboda bata taba tunanin zata samu irin wannan dakin ba tazata ko a kitchen zata na kwana hajiya tadafa kanta tareda fadin babu komai kinji kisaki jikinki da kowa tajuya tafita dakin tabi da kallo tana mamaki acikin ranta shiyasa mutane suke son zaman birni domin ko ba komai zaka samu muhalli mai kyau da wannan tunanin ta dauki dan kullin kayanta wanda ke daure acikin dankwali baifi kala shida ba tajefa cikin wardrobe din tajuya tafada kan gadon tana murna.

No comments

Powered by Blogger.