Header Ads

'YAN MATA GA KALMOMIN SO MASU RIKITAR DA ZUCIYAR SAURAYI

Gareka abin burina kai kadai ne na farkon shiga zuciyata kuma daga kanka na rufe kofa babu wanda zai samu mafaka. Rashin ka acikin rayuwata tamkar rashin ruhine a gareni kuma halartar kabari ya tabbata akaina jikina yana bani kamar yadda kake kai kadai a cikin zuciyata nima haka nike ni kadai a cikin zuciyarka. Na gasgata irin tsagoron sonka gareni da irin amanarka, madallah da samuwarka hasken ruhina. Hasken ruhina koda wasa ban taba ganin wani a cikin jinsin samari mai kyanka da irin adonka ba, ga daddadan lafuza masu kwantar da zuciya dasa nutsuwa. Zan damka maka zuciyata da gangar jikina, na baka soyayyata na baka ruhina, idanuwana sundade suna tsumayen son ganinka kuma bazasu dainaba harsai sunyi tozali dai kai. Kai ne My Sweethrt domin kana sani farin ciki, kai ne My Love domin kai nake so, kai ne My Choice domin cikin mazaje kai ne zabi na, kai ne My Darling domin kai ne nake son ka zama uban 'ya'ya na. KINA NEMAN KARI?

No comments

Powered by Blogger.