Header Ads

BAKIN ALKALAMI

Part 2 Wucewa tayi izuwa falo na biyu nanma babu kowa dan haka tawuce izuwa falo na uku ananne ta hango hajiyarta zaune kan kujera gefenta kuma wata matace kusa da ita wata yar yarinyace itama zaune ahaka cike da kasaita ta karasa garesu cike da fara'a hajiya ta dubeta wadda kana ganinta kaga wayayyiyar mace mai mutunta mutane tareda daraja dan adam shekarunta baxasu gaza 40 ba farace tas doguwa marar jiki ta dubi yar tata tace Hannah mai aikin danake nema ce yau aka kawo min! Awulakance ta kallesu ta dauke kai tareda bata rai tace wacece acikin su wadda zatayi aikin? Babbar ko karamar? Cikin sakin fuska matar tace ah karamar ce zatayi aikin ita wannan mahaifiyarta ce baki ta taba tace to amma banda girki zata nayi ko? Nanma matar murmushi tayi tace banda girki nice zan rinka yin girkina baki takara tabawa sannan tace to banda wanke wanke zatanayi ko? Dasauri matar ta kalleta tace haba Hannah wannan wacce irin magana ce? To idan banda wanke wanke me zatayi kinsan dai shi kadaine aikin da babu maiyi akwai masu shara akwai masu wanki dama gyaran falo da kitchen ne kawai babu masuyi,cike da gadara tace to hajiya saidai idan ke zata wankewa kwanuka amma nidai karta kuskura ta taba min dishes dina da kazamin hannunta ta barmin zan rinka wanke abuna dakaina tana kaiwa nan ta wuce batare da tajira taji abinda matar zata fada ba, matar tajiyo garesu cike da rashin jin dadi wanda ya bayyana karara akan fuskarta tace yafindo babu damuwa zata zauna tare damu nawa kika yanke zan rinka bata duk wata? Matar wanda aka kira da yafindo tace dama 3000 muka ce murmushi tayi tace to xan rinka bata 5000 amma dai sai tayi hakuri da hannah domin ni banajin kowa sai ita Hannah ita kadaice matsala da sauri matar tace babu komai sannan ta juya ga yartata wadda take zaune kanta asunkuye tana kallon kasa duk wadannan abubuwan da akayi bata ko daga kai ba tace ke Amna tun agida nayi miki fada kada naji kada naga ko rashin kunya ko daukar abinda ba abaki ba wlhi saina saba miki tana gama fadar haka tamike idonta cike da hawaye saboda rabuwa da zatayi da yar tata.

No comments

Powered by Blogger.