Header Ads

KALMAR SO DAGA BAKIN MASOYAN ASALI

Na kyautar da soyayyata ga wadda ta cancanta da wannan babbar kyauta;- =itace wadda idanuwa basa gajiya da ganin kyakkyawar fuskarta =itace wadda kunnuwa basa kosawa dajin zazzakar muryarta =itace wadda tafiyarta ke zama abar yabo da kallo a lokacin sassanyar iskar yammaci =itace wadda sautin muryarta idan ya ratsa dodon kunne sai aji kamar busar zazzakar sarewar aljanu =itace ma'abociyar yalwar gashin gira baki sidik da kyallin hakori da lotsawar kunci idan tayi murmushi

No comments

Powered by Blogger.