Header Ads

ILLAR ZURFIN CIKI A SOYAYYA!! WANNAN LABARI YA FARU DAGASKE BA KAGE BANE.

Wani yaro dan shekara shabiyar ya kamu da son wata yarinya dake makwabtaka da gidansu, amma yayi zurfin ciki bai sanar da ita ba. A haka suka taso tun daga kuruciyarsu har girmansu. Ya kasance a wannan hali har abin ya soma zama cuta a gare shi. Akwana a tashi, rannan sai matsanancin rashin lafiya ya kwantar dashi a asibiti. Likita ya sanar da mahaifansa cewa ba komi bane illa boyayyen ciwon zuciya ne da ya dade yana fama dashi, wanda yayi sanadiyyar lalata zuciyarsa. Wannan ya tabbatar da cewa rayuwarsa tazo karshe. Yarinyar tazo asibiti ta kalle shi,hawayen tausayi suka soma zuba daga idanunta sakamakon ta same shi a matsanancin hali. Sai yayi murmushi na karfin hali ya kalleta yace; Naso ace na nasan wanda zaki kasance dashi a matsayin mijin auren ki tun kafin na bar duniya, amma Allah bai nufa ba, gashi yanzu ya rage saura dan lokaci kadan. Sai ta amsa masa da cewa; Babu wanda na dade ina kauna kamar kai a duniya, yau ne ranar dana yanke shawar in fito in sanar dakai, amma sai gashi na same ka a wannan hali. Nan take ya tashi daga kwance yayi kokarin mikewa amma ina, ya yanke ciki ya fadi kasa babu matacce. Ba'a dauki wasu kwana ki ba itama aka same ta a kwance babu rai a jikinta,sai dai tabar wasika dake dauke da rubutu kamar haka "Bazan iya rayuwa ba in har baka a duniy" YA KAMATA MU DAI NA ZURFIN CIKI GA ABINDA MUKE SO. KADA KA/KI BAR ABINDA KAKE SO A ZUCIYA BA TARE DA BAYYANAWA BA, DON BAKA SAN ILLAR DA ZAI HAIFAR MAKA BA HAR SAI LOKACI YA KURE. Allah yasa mu dace.

1 comment:

Powered by Blogger.