Header Ads

BANDA DARIYA

A wani kauye ne wasu yara guda biyu suka saci mangoro a cikin buhu. Sai suka tsaya suna shawarar inda zasu je su raba ba tare da kowa ya gansu ba. Sai daya ya bada shawarar a tafi makabarta. Bayan sun isa makabartar dauke da mangoron nan, a daidai kofar shiga makabarta sai mangoro biyu suka fado daga cikin buhun, amma saboda suna sauri kada a gansu sai suka barsu nan suka wuce cikin makabartar da sauran mangoron. Suna shiga sai suka zube mangoron a kasa suka fara rabawa, babban ne yake rabo. Sai ya dauki daya ya sa a gabansa yace "Ni daya" sai ya kuma dauka ya sa a gaban abokin yace "Kai daya" a haka suka ci gaba da rabonsu. Can sai ga wani Dan shaye-shaye ya dawo daga wajen shaye- shayensa, yana zuwa daidai kofar makabartar da niyyar ya debi mangwaran nan da suka zube, sai yaji wata yar karamar murya kamar ta yara tana cewa kai daya ni daya kuma an cigaba da maimaitawa. Sai kuwa ya garzaya da sauri gidan limamin garin. Yana zuwa ya same shi a kofar gida yana shirin yin alwalar magariba yace alagafarta malam "yau wani bakon abu ne ke faruwa a makarbarta can naji ana rabon matattu". Sai liman yace "muje na gani". Suna zuwa sai suka labe a bakin kofar makabarta sai suka ji ana cewa kai daya ni daya...can sai suka ji ance kai ga yawan naka nima ga yawan nawa...can kuma sai suka ji ance. Toh wadancan biyun na bakin kofa fa? Sai suka ji daya yace toh muje adauko su mana. Haba!! Dajin haka sai mashayin nan da liman suka ari takalmin kare. Suna fadin ai mu ba matattu bane ai mu bamu mutu ba.. Lot of love (Lol). Kada kayi dariya kai kade

2 comments:

Powered by Blogger.