Labarin Soyayya Mai Ban Tausayi Na BARIRA da MUGHIR
******************************** Asalin Barira dai baiwa ce da kan kai ziyara wajen Uwar Muminai Nana Aisha (rta) matar Manzon Allah (saww). Barira baiwa ce ta Banu Mugira kuma tana da miji wanda shi ma bawa ne mai suna Mughir. Barira ta kasance fara ce Kyakykyawa Mijinta kuma Mughir ya kasance baki ne. Mughir Na Matukar So da Kaunar Barira a Ransa, Sai dai kuma ita Barira Bata kaunarsa ko kadan, tana zama da shine kawai don bata da yadda zatayi kuma gashi sun kasance dukansu bayine. Wata Rana Iyayen Gidan Barira Wato Banu Mugira suka CE da Barira zamu 'Yan tar da ke idan kika shekara 3 kina yi mana hidima. To A irin ziyarar da Barira ke kai wa Nana Aisha (rta), A cikin irin wannan shige da ficen da ta ke yi ne har ta sanar da Nana Aisha yarjeniyar da ke tsakaninta da iyayen gidanta na samun 'yanci bayan ta fanshi kan ta na tsawon shekaru 3. Lokacin da Nana Aisha (rta) ta ji haka sai ta sanya Barira tuntuban iyayen gidanta in sun yarda za ta biyasu kudi ta sayi Barira, a lokaci da Barira ta tuntubesu sai kuwa suka yarda, Nana Aisha (rta) Na sayen Barira sai ta 'yantar da Barira (sai ta zama 'ya). Bayan da aka 'yantar da Barira, to yanzu a tsarin shari'ar musulunci tana da zabi tun da ta zama 'Ya mai 'yanci. A lokacin da aka tambayi Barira zabin ko dai ta ci gaba da zama a karkashin mijinta wanda har yanzu shi bawa ne ko kuma a raba auren nasu. Barira taji farin ciki sosai da wannan zabi da aka bata. sai ta zabi a raba aure don ita dama ba son sa ta ke ba, ta yi hakuri ne ta zauna da shi a matsayin miji don lokacin ba ta da 'yancin yin hakan. Haka dai aka raba aure ba tare da son mijinta Mughir ba. Mughir ya shiga firgici da dimuwa da tashin hankali sakamakon irin tsananin soyayyar da yake wa Barira. Ibn Abbas YaCe: SAKO-SAKO, LUNGU da LUNGU, KWARARO-KWARARO na MADINA MUGHIR YA RIKA BIN BARIRA YANA KUKA YANA ROKONTA AKAN A MAYAR DA AURENSU ITA KUMA TAQI YARDA, SABODA BATA SONSA BATA KAUNARSA. Wata rana sahabbai (rta) suka ga irin halin da mughir ke ciki, suka cewa Manzon Allah (saww) shin baza ka shiga cikin al’amarin Mughir da Barira ba Ya Ma'aikin Allah?, Manzon Allah (saww) sai Yace, hakika anjarrabi Mughir da soyayyar Barira. Manzon Allah (saww) ya taka da kafarsa mai daraja, yaje wajen Barira da kansa Ma'aikin Allah (saww) sai ya kira Barira ya ce mata: "Da kin mayar da auren ku da mughir mana" sai ta ce: Umarni ka ke yi min ya ma'aikin Allah? Sai ya ce: "a'a Ni dai kawai ina nema masa ne". Sai ta ce: Ni kam bana bukata, ban son sa, amma in umurni kake min zan iya komawa. Haka Manzon Allah (saww) ya taso yana mamakin irin yadda zuciyar Barira bata nutsu da Mughir ba duk kuwa da irin yadda yake nuna soyayya da bege a gareta. Manzon Allah (saww) ya tausaya wa Mughir Sosai, har ma yake gaya wa Baffansa Abbas (rta); " Ya Baffa Shin baka mamakin irin wannan tsananin soyayyar da Mughir ke yi wa Barira, da kuma tsananin kiyayyar da Barira ke yi wa Mughir Ba?". Haka dai Mughir Ya kasance Cikin tsananin so da kaunar Barira ita kuma a duniya babu Wanda ta tsana kamarsa. DARASIN DA KE TATTARE A CIKIN WANNAN KISSAR; 1. Idan har mun nemi Macce ko macce ta nemi namiji da Soyayyah bata samu ba to Mu tuna da mughir, Kasancewa Har ma'aiki (saww) Ya je yi masa bikonta ammma taqi amincewa. 2. Iyaye Su daina tilastawa 'ya'yansu akan Auren dole, Domin Manzon Allah (saww) da ya bawa Barira Umurni to haka zata daure ta yi abin da ya ce, amma tun da ta fito da abin da yake cikin zuciyarta a fili, kuma bai tilasta mata hakan ba duk da tausayi da yake na Mughir. 3.Idan har kaga wani ko wata na wahala kan wani ko wata a kan SO to kaje ka nema masa soyayyar amma kuma kada ka takura akan dole sai anso mutum. Da ana haka da tuni Manzon Allah (saww) Ya sa Barira ta amince. 4. Kada iyayenka su CE dole sai ka aure wance ko dole sai ke auri wane, ki bijirewa Umurninsu, domin da Umarni Manzon Allah (saww) ya yi mata haka zata daure ta yi abin da ya ce, amma tun da zabi ya bata sai ta zabi mafita a gareta. Wannan Sakone Daga Zauren-Manazarta, Don Allah Ku Turawa 'Yan Uwanku, ko za'a samu fahimtar juna a wannan zamani.
No comments