Header Ads

WAYE YAFI IYA SATA???

wani saurayi da budurwarsa, suka shiga wani super market kuma ba bu mai ko kwandala. Gashi budurwar tana son shan chocolate. Suna fitowa ta kalli saurayinta ta ce, kasan duk kwampitar wajen nan sai da na dauki chocolate 3 ba,a ganni ba." Ka gani ma, ta nuna mai. Ya ce, "muje nima in dauko" suna shiga sai ya ce wa cashier din ka taba ganin an yi tsafi a gabanka?" cashier ya ce, "a'a" saurayin ya ce bari na gwada maka, miko min chocolate 1." ya miko mai ya sanye. "Karo wata" akai haka har sau uku yana kar6a yana sha. Yana gama shanyewa ya ce. "Bude jakar kwankwata kaga abin mamaki" yana budewa ya ga chocolate ukun data dauka. Waye yafi iya sata aciki???

No comments

Powered by Blogger.