Header Ads

******** MUHAWARA ********

Acikin wa'yan nan mutane guda 2 wayafi kwadayi? mutum na farko ya karbo kudinsa naira dubu dari! Daga banki, sai yazo wucewa ya taradda wani Alhaji yana rabawa mutane zakka, da mutumin nan yaga haka saiyaje ya boye kudinsa a wani lungu, yazo yabi layin karban kudi sai yayi rashin sa a kafin a,iso kansa kudin ya kare, yakoma inda ya ajiye nasa kudin ashe wani yagansa lokacin da yake boyewa yabiyo ya dauke.... Mutum na biyu kuma yaciyo dumamensa daga gida yafito sai ya taradda wasu mutane suna cin abinci mai rai da lafiya, ba kalar wanda yaci ba! sai suka ce masa bismillah sai yace musu toh ina zuwa, sai yaje wani lungu ya amayar da abinda yaci a gida da niyyar yazo yaci wannan abincin da aka masa tayi, kafin yadawo sukuma sun cinye da yadawo sai suka cemar ai sundauka bazai ci ba ne shyasa ya tafi. To a cikin wa'yan nan mutane guda 2 wayafi wani kwadayi?

No comments

Powered by Blogger.