Header Ads

WAYE GWANIN QARYA KUWA A CIKINSU ?????

BABBAR MAGANA 'Yan-mata Da Samarin Zamani : Wata rana wani gaye ya shiga mota daga Abuja zuwa Kano. A cikin motar sai ya ga wata kyakkyawar yarinya ce zaune kusa dashi. Su ka gaisa bayan ya zauna. Tun daga Abuja yarinyar nan keta faman latse-latse a wayarta. Tana yi ta na satar kallon gayen. Ashe shima gogan naku hankalin sa na wajen ta. Bayan an kwashi wajen awa daya (1hr) ana tafiya sai ya ja ta da fira, ga yadda firar ta kasance::: Gaye: amma 'yan-mata wayarki na da kyau. Wane model ne ? Yarinya: BB ce bold 15... Kaga wannan wayar water proof ce, ko cikin ruwa sai ka yi waya da ita. (Cikin ransa, sai gayen nanya ce "lallai yau karya ta gamu da karya") Shi ma sai ya fito da tashiwayar ya nuna mata) Gaye: kin ga ni kuwa tawa bold 20 ce, bata ma fito ba, sample ne BB suka aiko man don yawan sayen wayarsu da nake yi. (Yarinyar nan ta juyo tana kallon shi). Yarinya: Ita kuma wannan wayar me take yi ? Gaye: (Sai yayi murmushi) kin ga wannan wayar, ko daga ina ta fado ba ta yin kome. Yarinya: da gaske ? Gaye: kwarai kam...ai da ta fado sai parachute ya fito daga jikin ta ya bude, ahankali za ta sauka kasa, ta kuma gyara zama.. Yarinya: ni kuwa tawa wayarba ka missing call da ita. Gaye: Kamar yaya ? Yarinya: da an kira ka, ko barci ka ke sai wayar ta gungura ta gano ka don ka dauka. Gaye: (yayi shiru yana tunani, Can sai ya duka ya shafi takalminsa) kinga takalmin nan, dala dubu hudu ($4,000) ake saida shi. Yarinya: (Ta duka tana leqen takalmin dala dubu hudu ) Amma naga kamar ordinary takalmi ne. Gaye: (Sai yayi murmushi) Ai wannan takalmin in kina sanye da shi ko tuntube ba kiyi, da kinyi tuntube sai air-bag ta fito fyuu!!! Yarinyar nan sai ta bushe da dariya. Shi ma mutumin naku sai abin ya ba shi dariya... Yarinya: lallai yau na gamu da gamo na. Shin A Cikin Wadan Nan Mutanen, Waye yafi iya Karya ???

No comments

Powered by Blogger.