Header Ads

SHIN WAYAFI IYA YAUDARA CIKINSU

Wata rana wata budurwa taje gidansu 'kawarta sai ta had'u da wani Gaye, ga yanda hirarsu ta kasance. Saurayi- Salaam 'yan Mata ya sunanki? Budurwa- sunana Maryam tanayi tana satar kallonshi da gani ya kwanta mata arai. Saurayi- Ina ne gidanku? Budurwa- tai wuf ta nuna gidan 'kawarta, kasantuwar 'kawar tata masu kudi ne. Nan sukai musayar numbobi, kullum zai zo saiya kirrata, dan haka takan shirya ta tafi can gidan 'kawar anan suke zance, tayi hakanne dan ya dingai mata toshi da yawa karya ga gidansu na Talakawa ya dingai mata 'kananan kyauta.. Wata rana ba wataran ba sai akayi rashin dace wayarsa ba caji, a 'kofar gidan yaga wani yaro yace kai kiramun Maryam. Sai yaron yace yau bata zoba. Saurayi ya ce daga ina? Daga gidansu Yaro ya bashi amsa. Au daman banan bane gidansu? Yaro yai gaba yana cewa zo in kaika gidansu, basu 'karisa ba ya hangeta tana ta tuyar dankali, ga yara sun yayyabeta. Ya 'karisa ya tsuguna yace 'yan mata abani dankali, tana jin muryarshi ta dago suka hada ido, ta mike ta ruga gida aguje, daman gidan 'kasa ne, yace kidaina gudu ni tsakani da Allah nake sonki, daganan ya aika afada ma iyayenta gobe zai turo arushe gidan, ai musu 'kan'kararren gini na Zamani. haka kuwa akayi sai dai me? Tun randa aka rushe gidan ba Saurayi ba labarinnshi. Tambaya anan tsakanin Saurayi da budurwa waya fi iya yaudar

No comments

Powered by Blogger.