SANADIN BOKO 1-01
Na Maryam Abdullah K.Mashi Ina sauraren duk hirar da kowaccen su ke yi, motar ta kacame da surutu. Wasu na murnar ganin Iyayensu, wasu kuma suna zancen auren su. Mafi yawa daga ciki kuma suna fadin makarantun da za su ci gaba, wasu su ce poly wasu Jami'a, wasu Nursing school. Sa'adatu da ke kusa da ni ta ce, "Hafsy don Allah kema ki shigo (A.B.U Zariya) mu hadu mana." Nayi dan murmushin takaici. "Samun (A.B.U) fa ba kamar shiga Bakori ba ne, saboda in ma zan samun bani da wani tabbas akan za a barni." Ta zaro ido. "Kada kice min kina cikin wadanda za'a dakile a kai gidan miji? Na sake ajiyar zuciya. "Ke dai Sa'a taya ni da addu'a, Allah Yasa ina da rabo, dan kuwa ina son in ga karshen boko." Jamila ta dube ni, "Hafsy ko yaushe kina bani mamaki in kina cewa za ki ga karshen boko. To bari kiji, sai dai boko yaga karshen ki. Ance miki wannan lokacin yana jira ne? Na ce, "To Malama, ban saka bakin ki ba, ina ruwanki. Ke ba kince aure ba?" Jamila ta ce, "Aure kuwa insha Allahu ba ya hana karatu, zan yi aurena na ci gaba da karatuna. Sa'a ta ce, "Wahala ai daya za ki zaba, don da kin yi ciki za ki watsar da batun karatu. Na ce, "Dubu nawa akayi? Ai ni boko yanzu muka sa dan ba." Ta ce, "Shikenan, Allah Ya taimaki kowa kan niyyarshi ta aikhairi". Na ce, "Ga magana da za ki yi kawai, Amin". Da tafiya tayi tafiya, sai ka ji kowa shiru. Ni kam fargabar Babana nake yi, nasan inba wani ikon Allah ba, da wuya naje wata Makarantar. An sauke yan zariya, sannan mu yan Kaduna muka nausa hanya, motar makaranta da ke Bakori Katsina, ita ce ta debo mu zuwa gidajenmu, bayan mun yi bankwana da makarantar wato mun kammala. Gidanmu ya kaure da sowa, yara na ta murna "Ga Hafsat ga Hafsat". Innarmu ta fito da gudu ta rungume ni, ina ta dariya. Almajiran da suka dauko min kaya suka sauke, na ce, "Innarmu ba su hamsin". Ta kwance habar zani ta mika musu. Yaran gida suka taya ni da kaya zuwa cikin daki, matan gidanmu kowa sai sannu da zuwa suke min ina amsawa. Inna ta aje min kwano tare da cewa, "Alalar har ta huce". Ta dire min kofin ruwa na ce, "Har yanzu bata kare ba ne?" Ta ce, "Ta kare mana, ai tun kwanaki da Kawunku Bako yazo ya ce min cikin kwanakin nan za ku kammala, kullum sai na aje alalar sai dai in naga magariba tayi ne sannan in ba yara. Nayi dariya tare da cewa, "Innarmu kenan! Ina Yaya Ummar?" Ta ce, "Tun safe bai dawo ba, kin san nasai mashin da aka yi mana rabon gadon nan, Kawun ku Bako na kawo min kudin na ce a sai mishi mashin wannan yaran, tunda zaman banza yake, aikin gyaran wutar nan ba ko yaushe ake samu ba. Ina fama da kannan shi ina fama da shi. Na ce, "Kinyi dabara Innarmu, in yayi Achabar sai a rufa asiri". Ta ce "Kwarai kuwa. Ummi ta zo ta zauna kusa da ni, na ce "Ummi da ba ina ta kiranki kin ki zuwa ba? Inna ta ce, "Kullum sai ta ce Innarmu ina Auntyna?" Na rungumota a jikina ina cewa, "Gani na dawo". Ta rufe fuskarta, ita dole taji kunya. Cin alalata nake ina jin dadi ga ni ga Innata, ta ce "Kin zo a daidai bikin su Hajara da Sakina ya kusa". Na rike baki, "Inna har da Sakina?" Ta ce, "Eh! Na ce, "Uhm! Ni da so samu ne in ci gaba da karatuna ma". Innarmu ta ce, "Malam ne matsala, amma ko Nas din nan da 'ya'yan Kawunki suke yi ai zan so kiyi." Na ce, "Wane Nurse? Ni fa Jami'a nake so, burina in zama 'yar Media". Ta ce, "Me kenan? Na kafa kofin ruwa na daddaka, sannan na ajiye tare da cewa, " 'yar jarida mana! Sai dai matsalar kudi ne". Kai lomar alala da nayi baki, ta zo daidai da sallamar Baba, nan take naji wani daci tamkar na tauna madaci. Innarmu ta mishi sannu da shigowa, tare da shimfida mishi tabarma. Cikin fargaba na soma gaida shi, ga mamakina yau fuskar shi sake ya amsa, har da ce min "An dawo lafiya?" Na ce, "Lafiya lau". Innarmu ta ce, "Allah cikin ikonSa Malam yau dai su Hafsat karatun Sakandire ya kammala." Ya ce, "To dama tunda da mai sonta sai ta yi masa magana ya fito in hada su da Sakina in huta". Inna ta ce, "Anya kuwa? Ina ga daurewa da zaka sake yi ta tafi makarantar gaba da..." Wani kallo da ya mata shi ne ya dakatar da ita. Ya mike tsaye ransa a bace. "Na gaji da wasa da hankalina da ku ke yi, ba zan iya ganin Hafsa gandandan cikin gidan nan ba, duk wanda ya shigo ba zai bambance ta da matan gida ba, duk wata tana zubar da jini, ta zama Uwar mata. Wannan karon zamu yi tsiya da ku yanda bakwa zato. Wai menene cikin wannan bokon da ku ka nace mawa? Ina ce karatun gidan duniya ne?" Inna ta kufulo itama, ta ce, "To dama ka saba ka min tijara cikin gida gaban kowa akan Hafsa, tun da babu sisinka kasa ido, kuma karatu ba fashi. Ya ce, "To zan ga wanda ke auren wani, tsakanin ni da ke". Ya fita. Na dago ido da hawaye, takaicina ace kullum Iyayena basa rigima sai a kaina, bari Munnir yazo anjima, zan ce masa kawai ya turo manyansa ayi magana, ko ina dakin nasa zanyi karatuna. Ban dai fadi ma Innarmu kudurina ba. Na mike ina tattara kwanukan gabana, Inna kuma sai mita take, na ce "Innarmu ki bar batun haka, kinsan gidan nan da gulma, yanzu kowa ya baza kunnuwa yana sauraro". Ta ce, "Suyi ta sauraro din, ina ruwana. Iyaka dai mace tayi da ni naji mu kwashi 'yan kallo ni da ita". Na idar da sallar isha'i, ina zaune a gurin ina istigfari, wani yaron gidanmu yayi sallama, bai jira amsa ba ya ce "Innarsu Ummi wai ana kiran Hafsa a waje". Ta ce, "To". Na mike, nasan Munnir ne, don na aika masa da letter cewa na dawo. Na bude jakata na ciro turarena forever na fesa, sannan na sabi gyalena na fita. Tun kafin na karaso na jiyo kamshin turarensa. Yana zaune saman motarsa kirar (Toyota camry), baka wuluk, sanye yake da wando jean baki, rigarsa fara. Cikin farin ciki na isa gabansa, nayi masa sallama ya dago da kanshi daga wayar da ke hannunsa yana latsawa. "Babyna". Sunan da yake kirana kenan. Na ce, Na'am". Ya diro "Zo muje cikin mota." Na ce, "A'a mu zauna can". Na nuna mishi dakalin kofar gidanmu. Ya dan gyara tsaiwa, "Kin ce fa baki son Baba ya dinga ganina da kananan kaya, kin san dai in muna can zai ganni dole ko?" Na dan yi jim ina nazari. Hakika Baba na fada cewa Munnir ba dan mutunci ba ne, ya gane haka ne tun daga suturar da yake sakawa. Amma bana son shiga motarsa saboda ya cika son taba jikina.. Ya katsemin tunani da cewa. "Zo muje, na zo da muhimmiyar magana". Na ce masa, "Nima ina da nawa muhimmin zancen". Baya ya bude ya shiga, nima na shiga dayan gefen, sai dai ban rufe ba. Ya ce "Rufo kofar mana". Na ce, "Ka barshi haka ma ya yi. Ya kunna wutar motar, haske ya bayyana, ni da shi muka kalli juna cikin ido. Nayi saurin janye nawa idanun, domin wani abu da na ji yana bin jijiyoyin jikina. Ya ce, "Ina sonki Hafsy, ban san irin son da nake miki ba." Ya kama hannuna na kwace, tare da mai da su baya na ce, "Don Allah Munnir ka daina son taba jikina, haramunne fa". Ya ce, "Zamu fara ko? Haba Hafsy, ni ne fa zan aure ki. Ko yaushe ina son in gwada miki so sai ki yi ta ki, yaya ki ke yi tamkar wacce bata je makaranta ba? Sai ka ce ba *yar boko ba? Ni fa kullum ina fada miki ba zan auri mata muje kina min wani kunshe-kunshen jiki ba. Na bata rai, ya shafi kumatuna. "Small beby, dan yi murmushi. Ba kya yin kyau in kin daure fuska". Shikenan, ban san lokacin da murmushin ya subuce min ba, matsalar ina mutuwar son Munnir. Ya ce, "To fada min maganar kafin kiji tawa, don tawa in kinji saikin bani goron albishir. Na ce, "To ni dai dama ina son ne in ce maka ya dace yanzun muyi aure, don wallahi da kyar Baba ya bari na gama karatun nan. Sam shi ba ruwan shi da da boko, ka dai sani". Ya ce, "Haba Baby, aure fa ki ka ce? Kin manta alkawarin da muka yi ni da ke?" Na ce, "Ban manta ba". Ya ce, "To ki kyale fadan Baba kawai, ba nine ke biyan komai na karatunki ba? Come on aje wannan topic din. Na shirya miki gagarumin party ne saboda murnar gama karatunki, don haka yaushe zamu je kasuwa musai kayan sawa? Takaici ya cika ni, don haka ban tanka ba. Ya sake matsowa in banyi magana ba nasan zai iya cewa zai rungume ni. Da sauri na ce, "Duk lokacin da ka shirya". Ya ce, "Gobe yayi? Dan ranar sati ne party din." Na ce, "Um". Ya ce, "Wai ba ki murna ne angel dina? Kada ki damu, kwanan nan za ki zana (JAMB), sai kin zama *yar media insha Allah. Na dube shi, "Yanzu sai zuwa yaushe zamu yi aure?" Ya ce, "Mun kusa, ai shekara hudu ya rage min na hada master dina, before time din kin zama *yar media ko? Nayi shiru. Ya sake matsowa har muna jin numfashin juna, bakinshi daidai kunnena ya ce, "Kin san ina son aure nima tuntuni damuwa daya Dad dinmu shi ne yaki. Yayyena guda uku suna nan harda mace, kin sani dai ya ce duk sai sunyi master sun fara aiki balle ni. Na ce, "To sai yanda Innarmu ta ce". Ya ce, "Bana jin Inna, zata yarda". Ya sake yin kasa da murya "In dan yi kissing din kunnenki?" Naja baya tare da cwa, "A'a". Ya ce, "To bari na tafi". Yana magana yana kallon agogon hannunshi, "Zan kalli wasan Arsenal yau." Na ce, "Kai kam har yanzu kana nan da kallon kwallon nan." Ya ce, "Kema za ki koya in kinzo gidanmu". Nayi dan murmushi. Ina son Munnir, shi yasa zan jure na jira shi, amma Allah Ya sani ina son aure, don ina zaton ina cikin mata masu bukata.... Ya katse tunanina da cewa, "Ko kada in tafi ne?" na ce, "A'a kaje sai gobe". Ya ce, "Shikenan." Ya miko min wata farar leda. ""Gashi kisha, ice cream ne da fresh milk." Na ce na gode, amma don Allah ka daina yimin irin wannan dawainiyar. Innarmu ta dubi ledar bayan na ciro kayan ciki, ashe har da kayan tea. Ta ce, "Kai yaron nan baya gajiya da dawainiya. Ni da zai fito ayi auren nan tunda yana zon karatun kyayi can a dakin shi. "Inna nayi mishi wannan zancen ya ce min in kara hakuri." Kamar na fadawa Inna zancen party din gobe, sai na fasa don nayi imani ba zata barni ba, duk da tana son abinda nike so. Yau Baba dakinmu yake, don haka dakin Babah kishiyar Innarmu zamu kwana. Ina kwance kan yaloluwar katifata mu da Sakina, can kasa sauran kannena da aka musu shimfida. Ko wannan cakudin na daga cikin abin da yasa nake son in ganni a dakin kaina. Washe gari tun safe muka soma aikin alalar siyarwa da Innarmu ke yi. Misalin uku saura Nazifi ya shigo yana cewa, "Hafsa ga saurayinki a waje. Ko da bai ce na kira ki ba, nasan gurin ki ya zo. Dama tuni nayi wankana, ina sanye da riga da siket na atamfar (Java), gyale na sura na ce "Inna Munnir na kirana." Ta ce, "To." Na nufi waje kai tsaye. Yana sanye da kananan kaya kamar ko yaushe, ina isa ya budemin gaban motar na shiga, sannan shima ya shigo. Na gaida shi ya amsa tare da yiwa motar key, na ce, "Muyi sauri ban ce zamu fita ba." Ya ce, "To". Wani (Boutique) muka je, duk tsinannun kaya ne a gurin, shi dai ya zabi nashi, amma ni nace ban ga wanda ya yi min ba. Nan ya shiga jidar min, na bata rai tare da nuna mishi sunyi yawa. Ya ce, "To zabi wanda ki ke so." Na daga duka babu na arziki, siraran wanduna ne da *yan riguna, sai doguwar riga wadda in nasa da kyar zata wuce gwiwata. Na aje su gefe, na dube shi. "Duk ba su yi min ba". Ya bata rai sosai, "Tashi muje". Na kafa mishi ido. Ya ce, "Tashi mana". Cikin daga sauti na ce, "To, to naji zan amsa, amma ni na gane kamar zasu yimin kadan." Ya dan sassauto "Muje gidanmu ki gwada." Da sauri nace, "A'a zasu yi min." Yayi murmushi, sannan muka je ya biya muka shiga motarshi. Ya ce, "Muje mu dan sha Ice cream". Na ce, "A'a kai ni gida, Innarmu bata san na fita ba, kuma nasan zata sa a leka ni, fada kuma zata yi min". Ya ce, "To naji sarkin tsoro, ke dai kawai kina tsoro ne kada na cinye ki." Gabana yayi muguwar faduwa ganin Baba zaune a dakalin kofar gidanmu, na ce na shiga uku, ga Babana, ya ce "To menene? Ina jin mamakin ki wallahi. Shi yasa Dad din mu yake matukar burge ni, baya takura mana, shi dai in dai zamuyi karatun boko to duk abin da muka ga dama muyi. Kuma zai kashe mana the last kudin shi don muyi karatu. Na ce, "Uhm, don Allah ka tafi da kayan, na karba, amma ka fito ku gaisa. Tare muka fito daga motar, jikina har bari yake. Na nufi cikin gida, Munnir yayi gurinshi. Ina isa Inna ta ce, "Daga ina ki ke Malam ya shigo yana ta fada yaga lokacin da ki ka shiga mota? Na ce, "Um asibiti muka je dubo kanwarshi". Ta ce, "Shi ne ba za ki fada ba? Kin san fadan Malam, don Allah ki rufamin asiri kada ki ja min surutu sanadin bokon nan." Na ce, "Kiyi hakuri Inna." Ina rufe baki Babanmu yana shigowa, tun kafin ya karaso na jiyo muryarshi yana cewa. "Na fada maka kenan, in da gaske ka ke yi ka turo min manyanka. Shekara nawa ina ganinka a kofar gidan nan wai ku *yan boko, zaku ce min sai kun gama boko, to ban laminci wannan ba." Hanyar uwar daka nayi, don nasan yanzun ya make ni, ya ce "Ke *yar boko kinbi saurayi kasuwa ko? Inna ta ce, "A'a Malam asibiti fa suka je." Ya zaburo tamkar zai kai ma Inna duka, ya ce, "In ji wa? Wa ya fada miki?" Inna ta ce, "Ga ta nan." Ya ce, "Makaryaciya, to shi abokin yawon nata ya ce min daga kasuwa suke, duk ya rasa wanda zai ce ya raka shi kasuwa sai ke?" Inna ta tsare ni da ido, "Kasuwa Hafsa?" Nace, "Kuyi hakuri, ba zan kara zuwa ba." Tayi kwafa tare da ci gaba da yin aikinta. Baba ya ce "To wallahi ba zan yarda da gantali ba, wai ku *yan boko." Inna ta dube ni, "Ai gara ki saka min da haka. Tunda ni na jajirce ki samu karatun boko." Na ce, "Don Allah Innarmu kiyi hakuri, wallahi ba zan sake ba". Ta ce, "To me yasa ki ka min karya? Kin san dai na tsani a min karya, duk abin da ya faru nafi son gaskiya ko?" Na ce, "Na sani. Haka nayi ta bata hakuri, kun san Uwa, nan da nan ta sauka. Ta min fadan cewa kada na sake yarda na bi saurayi wani guri. Kwana daya, biyu ban ji daga Munnir ba, lallai Babane ya kore shi letter na rubuta na ba Nasirun gidanmu na ce ya kai masa. Tambayarshi nayi ko lafiya? Na jishi shiru. A bayan takardar ya rubuto cewa Babana ya kore shi, don haka shi ya hakura da ni. Na girgiza da jin wannan zancen, don ina son shi kullum burina na aure shi. Shi kadai nake jin sha'awa. Na rasa yanda zan yi ko satar jiki zan yi na je gidan su? Innarmu ta gane ina cikin damuwa, ta ce "Hafsat ba ki jin dadi ne? Na ce, "Ciwon kai ne yake damuna." Ta bayar da Naira goma a amsomin panadol." Da dare nace Innarmu zan je gidansu wata yarinya *yar makarantar mu, in amso wasu takarduna, ta ce, "Kar ki zauna, maimakon kije tun ido na ganin ido?" Na ce, "Ai dazun ciwon kai ke damuna." Ban yi wata kwalliya ba, kada ta gane, sai kawai na dan fesa turare. Na zari mayafi, gidan su Munnir da dan tafiya tsakanin mu saboda mu muna Rigasa ne Abuja Road ta kasa, su kuma suna Makarfi Road. Tun daga nesa na hango shi su da wani tsaye, ga motarshi gefe, ina zaton fita zasu yi. Sai na kara sauri. Daidai ya bude motar zai shiga na ce, "Munnir" Ya juyo da sauri, ya mai da motar ya rufe. Abokin nasa yana ciki, ya ce, "Beby lafiya?" Na jingina da motar, sannan na sauke ajiyar zuciya, domin na gaji. Sai dai kuma lokacin ne naga rashin hankalina. Yanzun ince mishi me? Na zo in bashi hakuri ko nazo biko? Ya sake cewa, "Me ya faru Baby? Na ce, "Ai ba ka ma sani ba?" Dabara tazo min, na ce "Dama nazo ne na maka godiya akan dawainiyar da kayi da ni, don ko zamu rabu bai dace mu rabu ba zumunci ba." Ya ce, "Baby kenan, don na fada kina ganin zan iya rabuwa daKe? Ni ina sonki, Babanku ne ya tozarta ni" Kafin nayi magana ya ce, "Ina zuwa." Ya leka motar yayi magana, sannan ya ce, "Zo muje ciki kiji." Na ce, "A'a. Ya bata rai, "Bana son yawan gaddamar nan, ki daina kada muyi aure mu zo muna samun matsala. Na ce, "Ina jin kunya ne, saboda Mamanku, Ya ce, "Ba za ta san kin shigo ba, zo muje. Na bishi, ya tura Gate din gidan, muka shiga. Yau ne na soma shiga gidansu, ginin zamani ne ga haske tamkar rana, me gadinsu ya ce, "A'a, ka fasa fita dinne? Ya ce, "A'a Baba, yanzun zan fita. Na gaida maigadin muka tafi ginin farko daga cikin gine-gine ukun da ke harabar gidan, ya ce, "Yau kin zo gidan mu, ba don kunya ba da na kira miki kannena su Nana. Na ce, "Barsu yanzun zan tafi, kuma bai dace su ganni cikin wannan yanayi ba, ina nufin shigar da nayi. Ya ce, "Shikenan. Katon falo ne, yana dauke da kayan more rayuwa, sai kofofi guda uku, yace in zauna kan kujera, na zauna. Ina kallon ko ina, ya nufi kofa daya daga cikin kofofin, jim kadan ya fito dauke da gwangwanin maltina da kofi ya zauna hannun kujerar da nike.
Jameelarh
ReplyDelete@Jameelerh ki gafarce ni Zuwa nanda lokaci kadan inshaa Allah
ReplyDeleteassalamu alaikum dan Allah ina son sanadin boko daga farkon na 4pls
ReplyDeleteassalamu alaikum dan Allah ina son sanadin boko daga farkon na 4pls
ReplyDelete@Khadijah kabeer ,
ReplyDeleteDan Allah hajiya khadeejah da jameelah kuyi mun uzuri Computer ta tasami matsala gashi wayatata bata Amma inshaa Allah zan saka muku Qarasa shen soon..... thanks you for being with us wish you to visit us again.
amincin allah yata bata agare mu dan allah inasan karashan wannan labarin
ReplyDelete@nana juwairiyya sadik,
ReplyDeleteki kara hakuri har yanzu banda waya ne sannan kuma system dita ta samu matsala..
Dan allah ainaxansami littafinnan
ReplyDeletemasha Allah
ReplyDeletemun gode allah yakara basira dan allah ka kokarta kacigaba da littafin
ReplyDeleteSlm nima ina son sanadin boko 4
ReplyDelete