Header Ads

SHARRIN BAN JI BA BAN GANI BA.

Wata rana Dila ya zo wajen Kura yace, kura Allah ya raba mu da sharrin ban ji ba ban gani ba. Kura tace kai dai Dila akwai 'danduniya, ta yaya mutum bai ji ba bai gani ba za a masa sharri? Dila ya sake cewa Kura Allah ya raba mu da sharrin ban ji ba ban gani ba. Kura ta ce kai tafi ka ban waje saboda shakiyanci irin naka kawai mutum bai ji ba bai gani ba sai a masa sharri. Dila ya kama hanya ya yi tafiyarsa, ashe zuwa yayi ya samu nakiya mai zaki ya saya ya je Fada wajen Sarki Zaki. Ya fadi ya yi gaisuwa kuma ya bayar da Nakiya ga Mai Martaba Sarki Zaki. Zaki yayi godiya, ya fara cin Nakiya, da jin zaki irin na Nakiya sai Sarki ya ce Dila ina ka samo irin wannan abu haka mai zaki? Dila yace Ranka ya dade wannan ai kashin Kura ne, amma idan haka ne kuwa kura bata kyauta ba, kamar kai yanda kake Sarki amma bata taba zuwa ta baka wannan kashi na ta ba? Nan fa Sarki ya fusata ya ce a je a nemo Kura. Tana ji an ce Zaki yana neman ta sai ciki ya duri ruwa. Ta tafi Fada ta fadi ta yi gaisuwa, Sarki ya ce Kura ina so ki min kashi. Kura ta ji abin bambarakwai haka, ta ce kashi kuma ranka ya dade? Yace eh kashi nake so ki yi. Dila ya lallaba wajen Sarki ya rada masa 'tana da taurin kai sai ta ji bugu take yi'. Da jin haka Sai Sarki ya sa aka fara jibgar Kura. Kura ta ji duka nan take ta fara kashi me doyi. Aka ce ta fara ta fara, amma bata yiyo mai zakin ba. Aka sake casa Kura, Kura ta ji duka yayi duka kawai sai ta fara gudawa. Da Dila ya fahimci Kura ta jigata duk ta yi la'asar, sai ya lallaba wajenta ya jefar da Nakiya. Sai ya ce yawwa! Ga shi ta yi! Sarki ya karba ya cinye ya sallami Kura, da kyar ta koma gida. Tana zaune tana jinya sai ga Dila ya shigo wajen Kura suka gaisa ya mata ya jiki ta ce da sauki. Dila yace: Kura Allah ya raba mu da sharrin ban ji ba ban gani ba. Da saurinta Kura ta ce: AMIN! AMIN!! AMIN!!! Dila.

No comments

Powered by Blogger.