Soyayya a Ma’aunin Shari’a
Ma’anar So: So ga bil adama shi ne karkatar zuciya da juyawarda izuwa wanda ake so, sakamakon wani abu da ya janyo karkatar zuciyar kamar kyon halitta, ko na dabi’u da halaye, ilimi da kwarewa a wani abu dss. Zuwa wanda take, ko yake so. Irin wannan so shi ake kira so mai dalili (Conditional love) Irin wannan so yana karuwa, kuma yana raguwa, sakamakon cancanzawar sababan da suke gudanar da shi. Akwai so da ake ce masa marar sababi (Unconditional love) Wannan irin so wasu suna ganin karya ne, wasu kuma suka ce cuta ne; shaidan ne yake sanya shi da izinin Allah a cikin zukatan da suka gafala, suka bar gurbin da shaidan zai cike shi da irin wannan nau’i na “so” zan ci gaba da wannan kasida nan gaba.ws
No comments