Header Ads

WA YA FI YAUDARA TSAKANIN MATA DA MAZA?

Manazarta da marubuta da kuma 'yan jarida sun ,sha yin rubutu ko rubuta littafai kan wannan batun. shine nima naga ya kamata in dan fadi al'barkacin bakina game da wannan batun mai daure kan gaske. to, a gaskiya a matsayina na na miji bai kamat in bada karfi a wani bangare ba.domin idan nayi hakan ya nuna akawi son rai kenan. baya ga haka ma to, a babin adalci ba hakan ya kamata ba.to, amma kasantuwar jin wadansu labarurruka na abokai. da na makota da kuma na 'yan-uwa da abokan arziki na kusa da na nesa da kuma jin abinda yake faruwa da wadansu mutane na daban. da kuma jama'an gari kila har da shaida wani abin a zahiri bisa kan hakan, to zai sa mutum yadan fhimci inda al'amarin ya sa gaba. to, ta hanyar ijn abubuwan da na ji ana fada idan yasu sai mai karatu { Mace ko namiji} su yi wa kansu hukunci kuma a ganina shine adalci. Zan fara da bangaren maza sau da yawa nakan ji wasu samari suna kokawa da kuma halin yaudara da kuma halin jari-hujja {Capitalisim} da wasu mata keda shi. har nakan ji suna cwa sau da yawa sai ka fara neman yarinya kun dade kuma ta riga ta shiga maka zuciya. daga bisani kuma suna ganin suna ganin wani mai kumbar susa ya zo sai kaga yarinyar tana neman hanyar da zata watsar da kai don ta kama wancan mai dan maiko-maikon. kuma a karshe koda ka kaiwa iyayanta wannan maganar sai kaga sun yi masa daukar sakainar kashi.{ kila ko duk kanwar ja ce}?daganan kuma kamar wasa sai kawai kaji maganar auran ya shiriricesaboda wancan shi ba mai kudi bane. wai har wsusu matan kance su fa idan ba mai mota bane ba za su iya aurensa ba. wasu kuma kance su gaskiya ba zasu iya zama a gidan yawaba.{ kila kuma ya gidan yawan babanta, da mamanta, da ita kanta suke}. wasumatan kuma ko da kuna tare idan har suks ji an fiye-yabonsu to, sai suji cewa sun wuce matsayin wanda suke tare da nufin aure.yanzu sai baban mutum mai kudi, mai gida da mota za'a aura.wanda amafi yawan lokuta hakan kansa wankin hula ya kaisu dare.daganan kuma sai a fara neman koma waye don kawai ana son ayi aure {an girma} ba wai don son wanda za'a aura ba. kawai sai ayi ayi aure don cimma wata manufa ta daban. kamar yadda nake ji kwanaki wasu suna fada wa mahaifiyarsu cewa ''su fa yanzu a gakiskiya sun fi son mijin da zai saka musu TV irin na jikin bango a falo, don yanzu shi ake yayi'' sai uwar tayi dariya tace ''kudai kuyi fatan inda zaku sami zaman lafiya da rufin asari'' to, kunga anan uwar ta nuna tasan ya kamat.kuma ta nuna wa yaranta cewa rufin asari da zaman lafiya shi ke kan gaba. a yayinda wasu iyayen babu ruwansu da wannan sai ma su bi ta yaran, aci gaba da cwa ai yanu kaza da kaza ake yayi. to idan akace haka za'a rika yi mai zai sa ba zaza'a rika samun matsala wajen auradda 'ya'ya mata ba? musamman ma 'ya 'yan talakawa. Ansan cewa babu ran da baya son jin dadi ko ni'imato., amma akan auna da yanayin da ake cikine, sai asa rai kuma anemi tai makon Allah {swa} gami da neman zabin Allah sa'annan kuma sai a zage damtse wajen nema. Akwai wat mace take cewa ''ai mafi yawan mata suna son su auri mai kudi, sai dai na wasu yafi na wasu ne kawai'' hakanan kuma na taba karanta wani labari a jaridar Aminiya cewa '' an taba fasa wani aure saboda rashin Naira dari uku 300. da aka bi bahasi lamarin wai ashe uwar yariyar ne ta ce wai babu atamfofi masu tsada a kayan auren kuma kuma kuma kudin sa lalle dabu daya zai biya shi kuma mijin ya ce shi dari bakwai zai biya 700, daganan dai auren ya fasu.wani hani ga Allah baiwa a karshe a garin aka baiwa wannan saurayin wata yarinyar wacce ta zarce wancan da komai. to anan don Allah wa ya ci baya? ba wai wannan bane kadai hanyar yaudara akwai wasu hanyoyi da dama da wasu matan da kuma wasu iyayan suke bi don yaudarar mutane.wanda mafi yawa kwadayine da kuma hali irinna jari-hujja {Capitalisim} ke jefasu cikin irin wannan mummunan aikin.wanda awadansulokuta harda hadin bakin iyayen musamman iyaye mata. sai ace wa yarinya wai '{ ki je ki samo mana na sabulu} amma wannan sai ina ganin kamar akawai gazawar wadansu iyayen musamman ma bangaren iyaye maza wajen sauke nauyin da Allah ya dora musu.da gangar ko kuma saboda yanayin da kasar ke ciki na La'ila'ha'ula'i [Allau wa alam} A bangaren maza kuma, suma mata suns fsdin al'barkacin bakinsu game da irin yaudarar da mazan keyi musu.kamar yadda na gane wa idona wani bawar Allah yana neman aure sau shida matan na yaudarasa.hakan nan kuma na gane wa idona wta yarinya kusan sau biyar maza na zuwa nemanta kai ka ce da gaske sukeyi. sai sun sa ta kori duk samarinta sai ka nemasu ka rasa.{ amma dai yanzu Allah ya taimaketa tayi auren} to, kaga irin wannan ba karamar mummunar hali bane.misali a garuruwan da ake bada kudin gaisuwa wato {nagani in so} to, wadansu lalatattun samarin sukan yi amfani da wannan damarne kawai don cimma burinsu,domin bukatarsu na biya shikenan don dama bawai sunzo da nufin aure bane na gaskiya. su kuma matan na wsu yankunan musamman arewa masu kudu dazaran budrwa taga an bada wannan kudin to, babu wanda zata kara sauraro sai wanda ya bada wnnan kudin {na gani ina so} wata yariyar kuma daganan duk abinda wannan bawan Allah ya ce ta yi to bazata yi masa gardama ba,don ganinshi zai aureta.Shi kuma gogan naka dama don haka ya bada wanna kyudin bawai don ya aureta ba.{kamar yadda wasu matan sukan fidda wanda zasu aura amma a gfef suna nan suna aikata masha'a da wani}. Tambaya;- shin idan wancan yariya yar { jari- hujja} ta ka sance irin matannanne masu matkar sonabin Duniya, kuma aka yi sa'a saurayi na da sakin hannu kwarai laifin wa zaka gani? Gaskiya akwai hanyoyin da wasu mazan kanyi amfani da su wajen jawo Hakalin mata musamman ma mata masu tsananin son abin Duniya. to, kuma dagananne komai ke faruwa.mama masu karin maganu sun ce { kuda wajen kwadayi akan mutu} to amma abisa gaskiyar zance a bangaren mata, lalle akwai masu yin wannan halin kawai don son rai.{'Ya'yan da iyayen} akwai kuma wanda gaskiya saboda iyayensu maza basa iya sauke nauyinda ya hau kansu na biyan musu bukatocinsu na rayuwa sakamakon matsanancin halin da aka jefa talakawa a ciki a kasar nan.{ amma kuma don ana matasanancin hali, ba yana nufin sai ayi amfani da wannan daman ayi ta sharholiya ba} Domin ta wani bangaren taluci kamar gwada imani ne. akan daure ne azama na kirki sai Allah ya kawo mafita.amma idan aka taru aka lalace saboda talaucin da aka sakamu ciki { Da karfin tsiya} to sai yaza babu fatan samun sauyi kanan 'Good hope' kuma hakan ba dai-dai bane { sauyi na zuwa nan ba da dadewa ba} insha'Allah. 1-Iyaye maza aji tsorn Allah wajen sake nauyin iyali iyakan iyawa! 2-Iyaye mata a ji tsoron Allah wajen bai wa yara tarbiyya da kuma fada musu gaskiya da kuma sa su a bisa turban abinda zai amfanesu Duniyarsu da lahirarsu. 3-'Yammata kuma a ji tsoron Allah a kuma rage kwadayi da kuma yawan son abin Dunuya sosai. komai na Allah talaka da mai kudi duk bayin Allah ne. babu wanda yafi wani a wuri Allah sai wanda yafi ijn tsoron Allah{swa|. kuma komai yanmada iyaka amma banda ikon Allah. kina iya auren mai kudin amma kafin shekar ta zagayo ya zama sai an taimaka masa da abinda zai sa acikinsa { Allah ya kiyaye} amin! to sai kice zaki fita? sa'annan kina iya hakuri ki dauki cewa komai na Allah neki je ki auri talaka wanda da kyar yake samun Abinda zaic, amma kafin shekara ta zagayo kiga ya zama hashakin mai kudi. { haka ya sha faruwa}a nan kuma me zakice, in ya zama da farko kin so ki kishi saboda shi talaka ne? don anyi hakan da daman gaske. 4-samari kuma don Allah aji tsoron Allah. a rika yin gaskiya wajen neman aure da sauran al'amura.idan ka yaudari 'yar wani to ko baka haifaba akwai sakayya daga Allah {swa} AL'KUR'ANI;- To, wanda ya aikata { wani aiki} gwargwadon nauyin zarra na alhairi, zai gan shi. aya ta 7 kuma wanda ya aikat gwargwadon nauyin zarra na sharri zai gan shi. aya ta 8. suratul zulzal. da fatan mun amfana

No comments

Powered by Blogger.