Header Ads

BAKIN ALQALAMI

Part 1 Bakar motace kirar zamani wadda masu hali suke yayi (Anaconda) ta tsaya abakin gate din makeken gidan dake unguwar General Muhammad Buhari Housing Estate dake cikin new G. R. A hon daya akayi wani matashin mai gadi ya taso da gudu ya bude gate din domin ko ba afada masa ba yasan waye hancin motar aka turo tashigo cikin gidan ahankali aka sauke bakin glass din motar wata kyakkyawar budurwa ce ta leko cikin sanyin murya kamar wacce take ciwon baki tace ina uniform dinka? Dasauri ya rissina yace ranki ya dade wankewa nayi kuma har yanzu bai bushe ba cike da yanga ta motsa bakinta tace idan nasake ganinka babu uniform sai ranka ya baci dasauri yace tuba nake ranki ya dade bata saurari abinda yake fada ba tamayar da glass din ta rufe taja motar izuwa cikin gidan wanda fadinsa yakai fadin rabin filin kwallo inda aka tanada domin ajiye motoci taje ta jera tata asahun yan uwanta dake ajiye wanda akalla sunkai kala 20 ahankali ta bude kofar motar ta ziro kafarta wanda take sanye cikin wani dogon takalmi mai mutukar tsini fitowa tayi wankan tarwada ce mai dan jiki duk inda ake bukatar cikakkiyar mace to takai kayan jikinta rigace doguwa Arabian gown tayane kanta da dan mayafin rigar shekarunta bazasu wuce 25 ba hannunta rike da wata fankaceciyar waya wanda tasa ear phone dinta acikin kunnenta ahankali take takawa kamar wacce take jin tausayin kasa,ko kuma ita tata kasar tafi ta kowa tsada cikin gidan ta hara gadan gadan ta bude kofar falon tashiga ahankali ta yi sallama wanda ba lallai ne wanda ke kusa da itama yajiba balle wanda ke nesa.

No comments

Powered by Blogger.