Header Ads

Wasa Kwakwalwa

Abokaina matasa da kananan yara ga wani wasa mai ban sha’awa da nishadi, da yake kaifafa kwakwalwa da saurin gano abu. Za’a iya yinsa a makaranta lokacin “break” ko a gida lokacin da ba’a komai Yadda tsarinsa yake: wadanda suke da sha’awar shiga wasan za su zauna wuri guda su jeru, ko su yi da’ira, sannan sai daya daga cikinsu ya tashi ya je can nesa; inda ba zai ji abin da za su fada ba, su kuma sai su hada-baki akan wani abu (mutum ko dabba, ko gari ko ma dai menene, amma ya zama sananne ne ga dukkaninsu, har shi wanda ya tashin ) sannan sai su ce masa sun shirya ya dawo, idan ya zo, shi kuma sai ya yi kokarin gano abin, ta hanyar tambayoyi; zai rika tambayarsu daya bayan daya, kuma duk wanda ya tambaya zai fada masa gaskiya, amma ba zai yi masa wani karin bayani ba, in kuma bai san amsar ba, sai kawai ya ce bai sani ba. Haka za su yi ta yi har sai ya gano, sai ya zauna, wani kuma ya tashi, idan ya dauki lokaci mai tsawo bai gano ba (kamar a yi zagaye uku, ko biyu gwargwadon yawan masu wasan, da yadda suka yi yarjejeniya, shikenan ya fadi sai a gaya masa) Saurin gano amsar yana da alaka da hazaka da kwarewarka\ki wurin ya tambaya. GA MISALAI *Wasu ‘yan mata ne a makarantar kwana, su goma bayan sun yi bitar karatunsu sun gaji, sai suka zauna don yin dan nishadi da wannan wasan, sai suka ce wacece za ta fara? sai Nusaiba ta ce ita za ta fara. Sai ta tashi ta tafi nesa, su kuma sai suka hada baki akan Nana A’isha matar manzon Allah (SAW) san nan sai suka kwalla mata kira ta dawo, ta zo ta same su sun yi da’ira tsaf, suka matsa mata ta zauna. Ta fara tambaya . Ta tambayi ta kusa da ita (wato ta daya) ta ce mata: mace ce ko namiji? Ta ce mace. Ta tambayi ta biyu tana raye ko ta mutu? Ta ce ta mutu. Ta tambayi ta uku; A lokacin Annabi (SAW) take ko bayan lokacinsa? Ta ce a lokacinsa take. Sai da ce yauwa! na fara gano bakin zaren! Sannan sai ta tambayi ta hudu: tana daga matan Annabi(SAW) ko ba ta ciki ? Sai ta ce a tana ciki. Sai ta ce da ta biyar: Mahaifinta shi ne babban abokin manzon Allah(SAW) wanda har Allah ya ambaci abotarsu a Kur’ani, ko ba shi ba ne? Sai ta ce shi ne. Sai ta ce Nana A’isha (R.A) Sai suka ce haka ne. Sai wata ta kuma tashi. Haka suka yi ta yi cikin nishadi. * Sumayya ita ce ta karshe, kuma da yake tana da kokari kwarai, ga ta gwanar tambaya, sai ta yi ta cika musu baki; tana cewa ita in ta yi tambayoyi da yawa ta yi uku za ta gano! Su kuma da suka fi ta, sai suka hada-baki akan ita Sumayyar, da ta fara ta yi ta yin tambayoyi ba kakkautawa amma ina! Duk basirar da take ji da ita ta kwakkwafe ta wai ko ta gano wanda ko abin da suke nufi ba ta gano ba, har daga karshe ta sallama ta ba da gari. Sai suka ce ai ke ce! Sai ta rike kai, ta yi kamar ta yi kuka, su kuma suka yi ta yi mata dariya suna cewa maganin mai cika baki kenan. Bayan sun ji garau sai suka koma kan muraja’arsu. * Nan kuma ‘yan samari ne suka je gidan su wani abokinsu ziyara, bayan sun ci abinci sai babar abokin nasu ta ce su yi wannan wasan, kuma ta gaya musu yadda ake yi. Sai suka fara. Ita kuma tana zaune tana jin su. Suka yi ta yi tana dada nuna musu dabarun yadda ake yin tambayoyi masu azanci. A karo na kusa da karshe sai suka hada- baki akan tsohon shugaban America George Bush uban shi wannan na yanzu. Da wanda ya tashi ya dawo sai ya fara canka. Ya tambayi na daya; dan adam ne ko ba dan adam ba ne? Ya ce dan adam ne. Ya tambayi na biyu: A nan gurin yake ko ba’a nan yake ba? Ya ce ba a nan yake ba. Ya tambayi na uku: ya taba rike wani babban mukami a rayuwarsa ko bai taba ba? Ya ce masa ya taba. Ya tambayi na hudu: musulmi ne ko kafiri? Ya ce kafiri. Ya ce da na biyar: Shugabancin kasa ya yi ko wani mukamin daban? Ya ce shugabancin kasa. Ya ce da na shida: A Amerika ne ko a turai ko a Afrika? Ya ce a Amerika. Sai ya ce Clinton! Sai aka ce a’a. Sai ya tambayi na bakwai; Yana raye ko ya mutu? Ya ce yana raye. Ya tambayi na takwas; lokacin da yake yakin neman zabe ya yi wa Amerikawa alkawarin cewa yakar musulunci ka’in da na’in shi ne daya daga cikin manyan ayyukan da zai sa a gaba in suka zabe shi? Ya ce ya taba fada. Sai ya ce George Bush Uban Bush na yanzu. Sai suka ce haka ne. Sai uwar ta ce to ai yanzun ma kamar shi ne yake mulkin, ko ma in ce gara shi, don kusan Amerika ba ta taba yin wawan shugaba, lusari makaryaci, mai nuna gabarsa ga musulunci da musulmi firi falo ba irin Bush na yanzu. Ya tashi haikan yana yakar musulmi da muslunci da sunan yaki da ta’addanci. A karshe Allah tona asirin kafiri; ya matsa bakinsa shi da kansa ya ce (Yakin Cross) yake yi (Ma’ana yaki da musulunci)! Dan karamin misali: Mutanen Iraqi MILYAN GUDA! Aka kashe a cikin shekaru biyar kacal da kasar ta yi karkashin mulkin mallakarsa! Amma har biki ya yi musamman larabar da ta fuce na cika shekaru biyar a Kasar! Kun gani ko ‘ya’yana! Don haka mu ci gaba da addu’a aniyarsu ta bi su, kulle-kullen da suke yi wa musulunci su koma kansu!‘ suka ce amiiin! Sai ta ce to yanzu sai ku tashi ku tafi gida kada a zo ana nemanku. Sai karamin cikinsu ya ce Umma to ai ni ban yi ba! Sai ta ce don Allah yi hakuri mantawa na yi. Bisimillah: suka hadu akan ZUMA, ita ma ta shiga cikinsu wannan karon, Da ya dawo ya fara ita: Matum ne, ko guri, ko abin ci, ko abin sha? Ta ce Abin sha. Ya ce da na biyu: A kwai abin da ya fi shi zaki? Ya ce babu. Sai ya ce zuma. Sai suka yi ta yi masa kabbara suka ce haka ne. Ita kuma ta kara masa da Naira 50 saboda bajintar da ya nuna wurinn saurin gano amsar, don kuma ta karfafa masa gwiwa. Yanzu kuma sai ku gwada.

No comments

Powered by Blogger.